An yi kira ga matafiya da su guji hawa motoci a kan hanya yayin tafiye-tafiye

Manhaja logo

Daga LAWAN MUSA a Bauchi

Shugaban tashar motocin da ke Awala ɓangaren ‘retain’, Malam Auwal Isah Ibrahim, ya yi kira ga matafiya da su ƙaurace wa al’adar nan ta zuwa bakin hanya su tare mota su hau, domin tsira da rayuwarsu.

Ya yi wannan kira ne a ofishinsa dake tashar motocin Awala Bauchi, makon da ya gabata.

Da farko ya gode wa Allah game da irin nasarorin da suka samu, “musamman haɗin kai da muka samu, bisa jagorancin tsohon shugabanmu Kwamared Abdullahi B. Muhammad, da Alhaji Isma’il Babawo, suka haɗa kai suka samar da haɗin kai a tsakanin mu, ‘yan retain da ‘yan ɓangaren N.U.R.T.W, ana zaune lafiya kowa yana gudanar da ayyukansa cikin lumana.

Kuma Ina gode wa Maigirma Gwamna, Sanata Bala Muhammad Abdulƙadir game da irin gudunmawar da ya bamu, na samar mana da jajirtaccen shugaba baki ɗaya, wato Alhaji Tijjani Baba Gamawa, wanda shi ma hakan ya ƙara samar mana da haɗin kai, babu abinda za mu ce sai dai mu gode wa Ubangiji.”

Sai ya koka game da babban ƙalubalen da yake ci musu tuwo a ƙwarya, na rashin wadataccen wuri: “Muna roƙon Gwamnatin Jihar Bauchi da ta taimaka ta samar mana da wadataccen fili da zai ba mu damar tafiyar da harkokin mu bisa tsari.

Domin yanzu haka yawancin motocinmu, wasu suna gidan mai, wasu suna bakin hanya duk mun ajiye su, ba mu da wurin kwana, ba mu da wadatattun banɗaki, duk da cewa Maigirma Gwamna ya yi mana alƙawarin samar mana da fili na musamman, kuma muna sa rai zai waiwaye mu nan ba da daɗewa ba,” inji shi.

Sai ya yi kira ga matafiya, musamman waɗanda ba su zuwa tashar mota, saidai su tafi wajen gari su hau mota, wanda ya nuna cewa hakan wata babbar matsala ce ga rayuwarsu, irin yadda ake kashe wasu, “mutum ne zai zo tasha, amma sai ya ce yana sauri ba zai iya jira ba, daga ƙarshe kuma shiga motar da ba a san ta su waye ba, ko kuma a yi hatsari a rasa daga ina gawar take.

Amma idan mutum ya zo tasha ko ba shi da komai muna taimakawa, kuma koda an samu matsala na hatsari, muna da yadda za mu kira ‘yan uwan matafiyin, wannan ya sa kusan dukkan mu shugabannin a bakin Awala muke wuni, saboda hana ‘yan gada-gada, kuma Alhamdulillah mun ga nasarar hakan. Saboda haka muna kiran mutane, su sani tasha wuri ne na kowa, duk abinda suke tunani ya wuce nan, da su je bakin hanya. Ko mutum ba shi da sisi, ya zo za mu taimaka masa,” inji shi.

Sai ya jinjina wa dukkanin ilahirin direbobin Bauchi, irin yadda suke bin doka da oda, “kuma Ina ƙara kiransu da su ƙara jajircewa kan wannan kyakkyawar ɗabi’a tasu. sannan mana da ofishin da muke ajiye duk wani kayan da aka mance da shi, wanda duk wanda ya mance da kayan shi zai zo ya duba, kuma a ba shi abin shi.”

Daga ƙarshe, sai ya yi addu’a, Allah ya dawwamar da zaman lafiya a Jihar Bauchi, har ma da ƙasa baki ɗaya.