Kisan Ummita: Kotu ta tura Mista Geng zaman gidan yari

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Kotun Majistare mai lamba 30 ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Hanif Sanusi Ciroma ta aike da ɗan ƙasar Sin ɗin nan Mista Geng zuwa gidan ajiya da gyaran hali sakamakon rashin hurumin da ta ke da shi na sauraron shari’arsa.

Yayin zaman kotun na ranar Laraba da ta gabata, lauyan gwamnati kuma mai gabatar da ƙara Barista Khalifa Auwal Hashim ya roƙi kotu da ta mayar da wanda ake tuhuma gidan gyaran hali a ajiye shi har sai an samu shawarwarin ma’aikarar sharia sakamakon cewar kotun ba ta da hurumi.

Ana zargin Mista Geng Qwarong da laifin kashe wata mace mai suna Ummukulsum Sani inda ake zargin ya yi amfani da wata wuƙa ya hallaka ta.

Sai dai bayan nazari kotun ta amince da buƙatar mai gabatar da ƙara ta tura wanda ake tuhumar gidan gyaran hali zuwa ranar 13 ga watan gobe na Oktoba domin sake gabatar da shi.

By Editor