Samar da bayanan sirri tsakanin al’umma na daga cikin aikin SearchWell – Darakta Saleh

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Ƙungiyar Bincike da Samar Zaman Lafiya da Cigaban Al’umma wato Searchwell for Community Peace and Development Network ta jaddada ƙudirinta na taimakawa jami’an tsaro don samar da ingantacen tsaro ga alummar Nijeriya.

Babban Daraktan ƙungiyar na ƙasa Bashir Saleh ne ya bayyana haka a zantawarsa da manema labarai a Kano ranar Talata da ta gabata.

Babban Daraktan ya ce babban aikin wannan ƙungiya shi ne karvar bayanan sirri daga wajen al’umma sannan su miƙa su ga jami’an tsaro.

Ya ce: “A cikin shekara guda da kafa wannan ƙungiya mun samar da bayanan sirri da dama kuma an samu nasarar daƙile su. Baya ga tsaro ƙungiyar tana sasanta matsaloli musamma na aure a tsakanin Musulmi da Kiristocin ƙasar nan, da sasanta gaba a tsakanin al’ummomi daban-dadan wannan ƙungiyar tana yi.”

Darakta Bashir Saleh ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tararayya da na jihohi da na ƙananan hukumomi da su fahimci cewa aikin tsaro ba aiki ba ne na jami’an tsaro su kaɗai ba, aiki ne na al’umma, don haka ya yi kira ga waɗannan hukumomi da su taimaka wa wannan ƙungiya da bada muhimmanci don samar da tsaro mai ɗorewa a faɗin ƙasar nan.

Detective Anas Umar wanda shi ne ADG a shiyya ta 5 da ke kula da jihohin Kano, Katsina, Jigawa, ya bayyana cewa baya ga taimakawa jami’an tsaro da rahotanni na sirri, ƙungiya ta na taimakawa wajen bada hannu a guraren cunkoso, ƙungiyar ta ware ma’aikatanta da ke kula da wannan.

Kazalika ya ce: “Muna taimakawa a fannin marayu da iyayensu suka mutu suka barsu, muna zagayawa a sibitoci mu biya wa wasu kuɗin magani, muna talkafawa ‘yan gudun hijira da kuma abinda ya shafi tsaftar muhalli da sauran abubuwa da dama wannan ƙungiya tana yi, ko a watannin baya ƙungiyar ta kama miyagun ƙwayoyi miliyoyin nairori inda ta damqa wa hukumar NDLEA ta Kano,” a cewar Detective Anas Umar.

Ƙungiyar SearchWell na da membobi aƙalla dubu 5 a ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano, kana ta na da membobi a kusan dukkanin Arewa da Kudancin ƙasar nan.

By Editor