Gwamnatin Nijeriya na shirin yin dokar da za ta hana cin ganda a faɗin ƙasar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa tana nan tana shirin ƙirƙoro da wata doka da za ta hana cin ganda a faɗin ƙasar

Darakta Janar na Cibiyar Fasahar Kimiyya da Sarrafa Fatun Dabbobi, NILEST, Muhammad Yakubu ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Abuja.

Ya ce dokar ta zamo dole domin a farfaɗo da harkar sarrafa fata a faɗin ƙasar nan.

Ya ce za a yi dokar ne domin farfaɗo da kamfanunuwan sarrafa fata a ƙasar nan.

A cewarsa, dole ne gwamnati ta hana cin ganda, wacce ba ta da wani amfani wajen gina jikin ɗan Adam.

Ya qara da cewa hana cin gandar da farfaɗo da kamfanunuwan sarrafa fata zai bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.

Ya ce akwai lokacin ma da a ka tava tura ƙudurin a majalisa kuma an tattauna a kansa ‘amma ban san ya a kai a ka ajiye shi ba’.

“Idan a ka tabbatar da dokar a majalisa, to tabbas za ta farfaɗo da kamfanunuwan sarrafa fata a ƙasar nan,” inji shi.