‘Yan Arewa mazauna Legas sun yi zanga-zangar ƙin jinin kwamishina da sunan Arewa

Daga JAMIL GULMA a Legas

Ƙungiyoyin ‘Yan Arewa Mazauna Birnin Ikko, sun aiwatar da wata zanga-zangar lumana bisa ga ƙin jinin Arc. Kabiru Ahmed wanda ke riƙe da muƙamin kwamishina a madadin ‘yan Arewacin ƙasar nan mazauna Legas.

Alhaji Ado Ɗansudu wanda yana daga cikin waɗanda suka gabatar da jawabai ya bayyana cewa ba shakka Arc. Kabiru Ahmed yana ci da gumin ‘yan Arewa mazauna Legas saboda bayan ayyana kansa a matsayin shugaba wanda sam ba haka ba ne saboda ba ya tare da kowa, bayan wannan yana yi wa ‘yan Arewa zagon ƙasa ta hanyar zaman wuƙa da nama wajen kai-komo tsakanin gwamnatin Legas da ‘yan Arewa ɗin ba tare da samun kowa ba.

Saboda haka akwai buƙatar a tsige shi tare da maye gurbinsa da nagartaccen ɗan Arewa da ke kishin ta wanda zai kare muradinsu.

Alhaji Muhammed Kudu Abubakar ya bayyana cewa bisa ga tabbataccen bayani Kabiru asalin sa a Ghana aka haife shi aka zo nan Agege da shi yana ƙaramin yaro a shekarar 1969 saboda haka suke ganin ba ya kallon kansa a matsayin ɗan Arewa ballantana ya yi kishinta da mutanenta.

Idan aka koma a bangaren jagorancin al’ummar Arewa mazauna Legas Alhaji Sa’adu Yusuf Gulma shi ne aka sani zaɓaɓɓe wanda kowa ya yarda da shi.

Honarabul Adebisi A. Yusuf da Honarabul Rotimi E. Olowo daga ƙananan hukumomin Alimosho 1 da Shomolu 1 su ne suka wakilci kakakin majalisar zartasawa ta jihar Legas Rt. Honarabul Musassiru Obasa inda suka karɓi baƙuncin ‘yan Arewar da hannu biyu-biyu sun kuma nuna jin daɗinsu bisa ga yadda suka tsara wannan zanga-zangar lumana ba tare da ɓarnatar da dukiyar al’umma ba.

Sun kuma bayar da tabbacin isar da saƙon ‘yan Arewan a wajen kakakin majalisa tare da ɗaukar duk matakin da ya dace ba tare da ɓata lokaci ba.

‘Yan jarida sun nemi jin ta bakin Malam Kabiru Ahmed dangane da zanga-zangar a harabar majalisar zartasawa da aka gan shi yana kai-komo amma dai hakan ba ta samu ba, haka-zalika wakilinmu ya kira shi ta wayar tarho amma wayarsa a kashe, ya kuma tura masa saƙon kar-ta-kwana shi ma har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton ba amsa.

Zanga-zangar da aka aiwatar ranar Litinin ɗin da ta gabata a harabar majalisar zartasawa ta jihar Legas da ke Ikeja dai ta sami halartar wakilcin matasa musamman ‘yan kasuwa daga kowane ɓangare daga cikin birnin na Legas da kuma Epe.