Dubun matar da ke safarar yara daga Kano zuwa Kudancin Nijeriya ta cika

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta ce ta kama wata mata a jihar da ta ɗauko yara tara a motar ɗaukar kaya, daga ƙaramar hukumar Ɗanbatta da ke Kano, ta nufi Jihar Ogun da su.

Yaran dai sun haɗa da masu shekaru 10 zuwa 15, kuma matar ta nufi garin Ijebu-Ode da je jihar Ogun ne da su, kafin a tare ta a jihar ta Kaduna.

Kakakin rundunar a Kaduna, DSP Muhammad Jalige, ya ce sun tare motar ce a shingen bincike na Kurmin Mashi, bayan sun lura babu taga ko ɗaya a jikinta, duk da cewa akwai mutane a ciki.

“Da misalin qarfe 4:00 na yammacin Lahadi ne jami’anmu suka kama motar.
“Daga matar har yaran ’yan Ɗambatta ne duka, kuma ta ce ta ɗauko su ne don taya ta sana’ar siyar da abinci da take yi a jihar Ogun,” kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kakakin ya ce za su ci gaba da bincike kan lamarin, kafin ɗaukar mataki na gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *