‘Yan Chana mazauna Kano sun yi Allah wadai da kisan da ɗan ƙasar su ya yi wa Ummita

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano

Ƙungiyar ‘Yan Kasuwa ta Al’ummar Sin mazauna Kano ta yi tir da kisan gillar da ɗan asalin ƙasar Sin ya yi wa Ummukulthum Buhari a ranar Juma’ar da ta gabata a gidan iyayenta da ke Unguwar Jan-bulo, ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano.

Wannan sanarwar na ƙunshe ne cikin takardar bayani da ke ɗauke da sa hannun mataimakin wakilin mutanen Sin mazauna Kano, Guang Lei Zhang, ta yi nuni da cewa Sinawa mazauna Kano bisa jagorancin Mista Mike Zhang ta yi tir da kisan gillar da ɗan asalin ƙasar Sin, Geng Quanhong ya yi wa budarwarsa.

“Aika-aikar abin a yi tir da ita ne, domin laifin ya yi kama da nuna ƙwarewa ta jami’an tsaro.

“A saboda haka, Sinawa mazauna Kano za su bayar da cikakken goyon baya kan a bar doka ta yi aikinta a kan ta’annatin,” kamar yadda aka bayyana a takardar.

Daga nan ƙungiyar ta yi na’am da karɓar baƙuncin Sinawa a Kano kuma sun yi alƙawarin kasancewa mutane nagari masu bin doka sau da ƙafa da abokantaka da bayar da gudunmawar bunƙasa tattalin arzikin Kano ta hanyar kasuwanci da cinikayya.

Sannan, ta miqa ta’aziyya a madadin Sinawa mazauna Kano ga iyalan Ummu-kulthum Buhari, saboda rashin ‘yar su da fatan Allah ya sayaya.

Ita ma daga vangaren Gwamnati Jihar Kano ƙarƙashin jagoranci Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta sha alwashin hukunta wanda ya aikata wannan aika-aika, kamar yadda iyayen marigayiyar suka buƙata na a hukunta wanda ya kashe ma su yarinya babu gaira babu dalili.

Haka zalika ma su rajin kare haƙƙin ɗan Adam ma sun yi iƙirarin yin tsayuwar daka don nema wa iyayen Ummita haƙƙin su na kashe ‘yar su da aka yi, inda da yawan malaman addini suka yi maganar cewa “ya kamata hankalin mai yankan kaba ya koma ga rina.”