Shugaban MOPPAN na Abuja, Auwal Falala, ya samu ƙaruwar ɗa namiji

Spread the love

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Allah Ubangiji ya albarkaci Shugaban Babbar Haɗaɗɗiyar ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Kannywood (MOPPAN) reshen Babban Birnin Tarayya Abuja, Hon. Auwal Sharif Falala, da samun ƙaruwar ɗa namiji a ranar Lagadi, 6 ga Afrilu, 2025, inda aka raɗa masa suna Muhammad Ashraf Falala ranar da aka yi taron suna bayan mako guda, wato Lahadi, 13 ga Afrilu, 2025.

Auwal Falala ya nuna farin cikinsa da samun wannan ƙaruwa, musamman ma kasancewar, jaririn da mahaifiyarsa suna cikin ƙoshin lafiya.

Baba Falala yana fitowa a finafinan Hausa masu ƙayatawar, wanda ya kasance ɗaya daga cikin jaruman fitacce fim ɗin nan mai dogon zango na Kwana Casa’in, wanda a ke nuna shi a tashar Arewa 24, inda Falala ɗin ya ke fitowa a matsayin kakakin majalisar dokoki.

By ukarofi