An yi taron Tarihi da Waƙoƙin Kassu Zurmi a Sakkwato 

Spread the love

Daga DAHIRU SAMA’ILA a Sokoto

Sashen Harsunan Nijeriya na Jami’ar Jihar Sakkwato da ke Birnin Sakkwato ya shirya Taron ƙasa da ƙasa akan tarihin rayuwa da waƙoƙin makaɗa Abubakar Kassu Zurmi. 

Taron na kwana huɗu ya gudana ne tsakanin Ranakun Jumu’a 18 zuwa Litinin 21 ga watan Afrilun 2025 a harabar jami’ar da ke Madorawa a birnin Sakkwato.

An buɗe bikin mai taken ‘Wawa Mugunyar Tsirfa’ Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi a Ranar Asabar 19 /04 2025 tare da samun halartar masana da manazarta daga ciki da kuma wajen Nijeriya.

ɗan majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar Mazaɓar Maru da Bunguɗu ta Jihar Zamfara a Majalisar Wakilai ta Tarayya, Honarabul Abdulmalik Zubairu (Zannan Bunguɗu) ne ya ɗauki nauyin gudanar da shi.

A jawabinsa shugaban majalisar gudanarwar jami’ar wanda kuma shi ne shugaban taron, Ambassada Abubakar Muhammad Sani (Makaman Sakkwato) ya bayyana muhimmancin taruka irin wannan da ke da zummar taskace lamurran rayuwar kiɗa da waƙa na mashahuran mawaƙan baka na Hausa domin zaƙulo irin woɓɓasarsu wajen ciyar da Adabin Hausa gaba.

Shugaban taron da ya samu wakilcin Farfesa Bello Bada, memba a majalisar gudanarwar jami’ar ya yaba wa hukumar jami’ar akan hangen nesanta na haɗa wannan taro da ya ce zai amfanar da al’umma ga bakiɗaya.

Yayin da ya ke maraba da mahalarta taron, Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa M B Yerima ya jefa wa sauran sassan da ke jami’ar ƙalubale da su zage damtse domin koyi da takwaransu wato Sashen Harsunan Nijeriya wajen ganin sun shirya irin wannan taro da ke da manufar ƙara fitowa da jami’ar sarari ta fannin ilimi, ya kuma bayar da tabbacin ci gaba da taimakawa ta wannan ɓangare.

A nasa jawabin, baƙo na musamman Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko (Sarkin Yamman Sakkwato) wanda shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin Jihar Sakkwato, Alhaji Bello Idris Chimmola ya wakilta ya bayyana taron a matsayin wani kadarkon cika giɓi da masana da manazarta ke amfani dashi domin magance ƙishirwar al’umma a fannin adabi. Ya kuma bayar da kyautar wasu littattafai da ya ɗauki nauyin wallafawa a cikin Harshen Hausa zuwa ga jami’ar a matsayin tasa gudunmuwa ga ɗalibai da sauran al’ummar jami’ar.

Sarakunan Zurmi da ƙaura Namoda daga Jihar Zamfara, Alhaji Muhammad Bello Suleiman da Alhaji Muhammad Sanusi Muhammad Ahmad Asha da Galadiman Garin Sakkwato da kuma Sarkin Sudan na Wurno daga Jihar Sakkwato, Alhaji Aliyu Attahiru da Alhaji Kabiru Cigari Alhassan jaddada goyon bayan Sarakunan gargajiya ne wajen ganin an farfarɗo da wannan fanni na waƙoƙin makaɗan baka da ke fuskantar barazanar zamani.

Yayin da ya ke nasa jawabin, babban baƙo mai jawabi Farfesa Balarabe Zulaydaini na Jami’ar Maiduguri, ya bayyana Marigayi Makaɗa Alhaji Abubakar Kassu Zurmi a matsayin shahararre kuma fahisin makaɗi da ya yi zarra a fagen waƙoƙin maza.

Shi ma a nasa jawabi, shugaban Tsangayar fasaha na Jami’ar Jihar Sakkwato, Farfesa Sirajo Mohammed ya yaba wa ɗan Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar Mazaɓar Maru da Bunguɗu a Majalisar Wakilai ta Tarayya, Honarabul Abdulmalik Zubairu (Zannan Bunguɗu) akan rawar da ya taka wajen ganin taron ya gudana a cikin nasara. Ya yi kira ga masu hannu da shuni da ke cikin al’umma da su yi koyi da wannan ƙoƙari na ɗan majalisar.

Hon. Abdulmalik Zubairu (Zannan Bunguɗu) wanda ya ɗauki nauyin gudanar da taron kuma ya samu wakilcin mai bai wa minista a Ma’aikatar Tsaro ta ƙasa shawara akan harkokin siyasa, wato Alhaji Ibrahim Maigandi ɗanmaliki Gidangoga ya nanata ƙudurinsa na ci gaba da bayar da gudunmuwa ta wannan hauji domin ceto Adabin Hausa daga taɓarɓarewa.

A jawabinsa na godiya, shugaban Sashen Harsunan Nijeriya na Jami’ar, Dakta Abdullahi Yunusa ya gode wa dukan waɗanda suka taimaka wajen samun nasarar taron.

An gabatar da manyan muƙalu guda uku da Farfesa Yakubu Aliyu (ɗanmasanin Gobir) na Sashen Harsunan Nijeriya a Jami’ar Usmanu ɗanfodiyo Sakkwato da Ibrahim Muhammad ɗanmadamin Birnin Magaji na fadar Mai Martaba ɗan Alin Birnin Magaji, Jihar Zamfara da Malam Abubakar Sani Sayaya na Iyatanci, ƙofar Sauri, Katsina suka gabatar akan fanni daban daban na rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi a ranar farko, wato Asabar 19/04 /2025.

Masana fiye da 70 ne daga sassa daban daban na Arewacin Nijeriya da Jamhuriyar Nijar suka gabatar da muƙalu daban-daban a wajen taron.

An kuma gayyato zuriyar Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi da suka haɗa da ɗiyansa; Malam Namakka da Malam Rabi’u da Malam Aliyu da jikansa Saifullahi da kuma halifansa a sabgar kiɗa da waƙa, Alhaji Mande Garba Sangamawa da kuma Makaɗa Zayyanu Garba ɗanwasa Gummi domin nishaɗantar da mahalarta taro.

Wani abin ƙarin birgewa game da wannan taro dai shi ne, yadda aka ɗabaƙa kalmar nan ta ‘Alheri gadon barci’, ko baka kwanta ba, naka ya kwanta, abin nufi anan, a wannan taron, iyalan marigayi Kassu Zurmi sun lashi zumar nishaɗantar da al’umma da mahaifinsu ya jima yana yi, inda suka samu kyautar maƙudan kuɗaɗe daga hannun Honarabul Abdulmalik Zubairu (Zannan Bunguɗu) da Ministan ƙasa a Ma’aikatar Tsaro ta Tarayyar Nijeriya, Alhaji Bello Muhammad Matawallen Maradun MON.

A ɓangaren Makaɗa Garba ɗanwasa Gummi da Makaɗa Alhaji Mande Garba Sangamawa Zurmi, suma ba a bar su hannu Rabbana ba, inda suka ribantu da kyautuka daga mutanen da muka ambata a sama.

Daga ƙarshe taron ya watse a ranar Lahadi 20/04 /2025, yayim da mahalarta taron suka kama hanyar komawa garuruwansu da ƙasashensu ranar Litinin 21/04 /2025, cike da gamsuwa da yanayin yadda aka gudanar da taron cikin ƙwarewa da kuma tarin ilimin da suka kwankwaɗa tare da fatan Allah Ya maimaita.

By ukarofi