Shugaban NLC ya yi buris da gayyatar ƴan sanda kan zargin ɗaukar nauyin ta’addanci

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Ƙasa (NLC), Joe Ajaero ya ƙi amsa gayyatar da rundunar ƴan sanda ta yi masa kan zarginsa da hannu a laifukan ta’addanci.

Rundunar ƴan sandan ta gayyaci Ajaero ne zuwa offishinta don amsa tambayoyi game da zarginsa kan ɗaukar nauyin ta’addanci, sata ta yanar gizo da sauran su a ranar Litinin.

Cikin wata takarda da tawagar lauyoyinsa ta fitar, Ajaero ya ce ba zai samu damar halartar ofishin ƴan sandan ba a ranar Talata, 20 ga watan Agusta, 2024 kamar yadda rundunar ta buƙace shi sakamakon ayyuka da su ka masa yawa, ya na mai cewa zai samu zuwa a ranar Laraba, 29 ga watan Agusta, 2024.

A gefe guda, cikin takardar da rundunar ta fitar ta ofishin sashen leƙen asiri ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Kwamishinan ƴan sanda, ta ce matuƙar Ajaero bai zo ba kamar yadda ta buƙata, to za ta kama shi.

Haka nan, tawagar lauyoyin Ajaero waɗanda ƴan ofishin Falana ne sun tabbatar da cewa shugaban NLC’n a shirye ya ke ya bada haɗin kai wa rundunar.

Sannan ta buƙaci hukumar ƴan sandan ta gabatar ma ta da cikakken bayani game da ababan da ake tuhumar sa akai la’akari da ƴancin haka kamar yadda dokar ƙasa ta tanadar.

By Babaji