Daga AISHA ASAS
Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Kwalliya na jaridar Blueprint Manhaja. Fatan muna lafiya tare da iyalanmu.
A yau darasin namu zai karkata ne kan abinda ba kasafai muke ba shi muhimmanci ba, wato shan ruwa akai-akai, maimakon haka, mun mayar da shan ruwa kawai a lokacin da muka ji ƙishi, idan ba mu yi buƙatar sha ba, za mu ɗauki tsayin lokaci kafin mu kai ruwa cikinmu.
Shan ruwa na ɗaya daga cikin manyan ababen da ke taka muhimmiyar rawa a lafiyar gangar jiki, rashin su kuwa kan haifar da matsala da dama.
Anan ina so mai karatu ya fahimci wani abu, idan na ce rashin ruwa, ba ina magana ne kan ruwan da muke sha a lokacin da muka ji ƙishi ba.
Anan ina magana ne kan yawan shan ruwa akai-akai koda kuwa ba mu yi muradin yin hakan ba, musamman ma a lokutan zafi wanda ruwan jiki ke saurin ƙonewa. Duk da cewa, ba a iya lokacin zafi ne jiki ke buƙatar ruwa ba, domin a lokacin sanyi ma ya kamata a mayar da hankali sosai wurin ganin an sha ruwa masu yawa, kasancewar ba a cika jin ƙishirwa a lokacin ba.
Yana ɗaya daga cikin ababen da ke taimaka wa wurin ƙarin bushewar fata a lokacin sanyi.
Na san da yawa sun san cewa rashin ruwa a jiki kan haifar da cutar bushewar fata da ka iya haddasa tsagewar ta, saidai kaɗan ne suka san ba a iya fata rashin ruwa ke taɓa wa ba.
A dalilin rashin ruwa, za a iya haɗuwa da cututtuka da dama, kamar yawan ciwon kai, kasala, rashin saurin narkewar abinci wanda ka iya haifar da yawaitar bushewar ciki da sauransu.
Idan kuma rashin ruwan ya yi ƙamari, zai iya zama babbar barazana ga lafiyar jiki, ta hanyar haifar da wasu daga cikin manyan cututtuka kamar tsakuwar ƙoda, matsalar fitsari, har ma yakan iya taɓa zuciya da dai sauransu.
Wataƙila mai karatu zai iya fakewa da shan kayan zaƙi na ruwa, kamar lemukan kwalba ko na roba, fura, kunu da sauransu a matsayin shan ruwa isashshe a wunin rana. Saidai abin lura anan, dukka ababen da na lissafa da ma waɗanda ke da alaƙa da su ba za a kira su da ruwa ba, duk da a nau’in ruwa ne.
Anan ina magana ne kan fafaren ruwa, waɗanda muke siya na leda ko na roba, ko na rijiya ko na fanfo.
Abin tambaya anan shin ya za mu iya gane jikinmu ba ya da isasshen ruwa?
