Shugaban SUBEB a Katsina ya ba mutane 727 tallafin kuɗi kimanin Naira miliyan 18

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mutanen da suka amfana waɗanda ‘yan asalin ƙaramar hukumar Kaita ne sun haɗa da malamai, limamai, hakimai, magaddai,masu unguwanni.

Saura sun haɗa da kungiyoyi su NULGE,NUT, ƙungiyar direbobi da na matasa maza da mata.

Akwai kuma masu ruwa da tsaki na jam’iyar APC a ƙaramar hukumar da sauran shugabannin jam’iyar a matakai daban daban.

A jawabinsa, shugaban SUBEB a Katsina Dr Kabir Magaji Gafiya wanda ya sassaka tallafin ƙarƙashin gidauniyar sa, ya bayyana cewa ya bada wannan tallafin kuɗi ne domin alummar yankin su sami abin sayen kayan masarufi ganin azumin watan Ramadan na ƙaratowa.

A shekarar da ta wuce sai da ya bada irin wannan tallafi ga mutane 557 ‘yan asalin ƙaramar hukumar.

Ya yabawa gwamna Dikko Raɗɗa kan abubuwan alheri da ya kawo wa ƙaramar hukumar wanda ya bayyana cewa tun lokacin mulkin sojoji rabon da a sami irin wannan cigaba a yankin.

Sakataren gwamnatin jihar Barista Abdullahi Garba Faskari wanda ya wakilci gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya yaba wa Dr Kabir Magaji kan yadda ya kawo cigaban ilimi a ƙaramar hukumar Kaita da jiha baki ɗaya.

Haka kuma ya yaba masa kan wannan tallafi musamman lokacin da ake shirye shiryen fara azumi watan Ramadan.

Shima Hakimin Kaita Alhaji Yazid Abdulkadir Kabir Usman ya yabawa gwamna Dikko Raɗɗa da shugaban SUBEB waɗanda ya ce sun raya harkokin ilmi a ƙaramar hukumar.

Masu bukata ta musamman a ƙaramar hukumar su ma sun amfana da tallafin kuɗin.

By ukarofi