Isra’ila da ƙungiyar Hizbullah da ke da sansani a Lebanon sun cimma yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta na kwanaki 60.
An fara tsagaita wutar ne da ƙarfe 4 na safe agogon GMT a ranar Larabar nan a daidai lokacin da ake fargabar ko tsagaita wutar za ta kai ga kawo ƙarshen faɗan da ake yi tsakanin sojojin Isra’ila da dakarun Hizbullah na dindindin.
Shugaban Amurka Joe Biden ya ce, yarjejeniyar za ta haifar da “ɗage tashin hankali na dindindin”. Biden ya ƙara da cewa, Amurka za ta sake jagorantar wani yunƙuri na tsagaita buɗe wuta a Gaza.
Masu shiga tsakani sun bayyana yarjejeniyar Isra’ila da Hezbollah a matsayin ginshiƙi na tsagaita buɗe wuta.
A cikin wannan lokaci, ana sa ran mayaƙan Hezbollah za su ja da baya a nisan kilomita 40 daga kan iyakar Isra’ila, tare da janye sojojin ƙasa na Isra’ila daga yankin na Lebanon.
Sa’o’i kaɗan kafin yarjejeniyar, sojojin Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai a kan iyakar kudancin birnin Beirut sau 20 cikin mintuna biyu, inda ƙungiyar Hizbullah ta ce, ta harba jiragen yaƙi mara matuƙi zuwa Isra’ila.
Harin na Isra’ila wanda aka yi a ranar Talata, yayi sanadiyyar mutuwar mutane 25 a ƙasar ta Lebanon.
Duk da yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta, Isra’ila ta gargaɗi mazauna garin da faɗan ya raba da muhallinsu da su guji komawa gidajensu, inda ta ce da sauran lokaci kafin hakan ta faru.
Isra’ila da Hezbollah sun tsananta musayar wuta ta sama a cikin watan Agusta. Sojojin Isra’ila sun fara mamaye ƙasar Lebanon kusan watanni biyu da suka gabata.
A ranar 25 ga watan Agusta, rundunar sojin Isra’ila ta ce, jiragen yaƙinta 100 ne suka ƙaddamar da hare-hare a kan ƙasar Lebanon bayan gano cewa Hezbollah na shirin harba makamai masu linzami da rokoki zuwa yankin Isra’ila.
Isra’ila ta ce, jiragen sun “harba tare da lalata dubban gangunan harba makamin roka” a wurare da dama a Lebanon. Jim kaɗan bayan kai hare-haren daga Isra’ila, Hezbollah ta ce, ta harba daruruwan rokoki da jirage marasa matuƙa zuwa cikin ƙasar Isra’ila.
ƙungiyar ta ce, ta harba roƙoƙi sama da 320, inda ta ƙara da cewa “kashi na farko” na harin da ta kai wa Isra’ila ya kammala.
Ta ce, hare-haren na ramuwar gayya ce ga kisan wani babban kwamanda da Isra’ila ta yi a Beirut. A tsakiyar watan Satumba, an ba da rahoton mutuwar aƙalla mutane goma sha biyu tare da raunata kimanin 2,750.
An zargi Isra’ila da laifin fashewar Pager:
Pager shi ne, na’urar sadarwa marar amfani da waya wanda ke karba da kuma nuna saƙonni. Hezbollah na amfani da shafukan yanar gizo a matsayin hanyar sadarwa mai sauƙi da rikitarwa don gujewa bin diddigin Isra’ila.
A halin da ake ciki, shugabannin ƙasashen duniya sun yi maraba da yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta tsakanin Isra’ila da Hezbollah.
Tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Lebanon za ta kare Isra’ila daga barazanar ƙungiyar Hizbullah da ke samun goyon bayan Iran tare da samar da yanayin zaman lafiya mai ɗorewa, inhi shugaban Amurka, Joe Biden, da shugaban Faransa Emmanuel Macron gabanin fara aiki da tsagaita wuta.
Sanarwar da aka fitar a ranar Larabar nan ta kawo ƙarshen faɗan da ake yi a ƙasar Lebanon, da kuma tabbatar da tsaron Isra’ila daga barazanar ƙungiyar Hizbullah da sauran ƙungiyoyin ‘yan ta’adda da ke aiki daga ƙasar Lebanon.
Amurka da Faransa za su yi aiki “don tabbatar da an aiwatar da wannan tsari sosai” da kuma jagorantar ƙoƙarin ƙasa da ƙasa na “gina ƙarfin” sojojin Lebanon, inji su.
Biden ya yi maraba da yarjejeniyar a matsayin “labari mai daɗi” ya kuma ce Amurka za ta jagoranci wani sabon yunƙuri na tabbatar da sulhu tsakanin Isra’ila da ƙungiyar Hamas ta Falasɗinu a Gaza.
Macron ya ce, ya kamata yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta ta Lebanon ta “buɗe hanya” don kawo ƙarshen yaƙin Gaza.
Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya gode wa shugaban Amurka Biden saboda “hannunsa wajen tabbatar da yarjejeniyar tsagaita wuta.”
Ya shaida wa Biden a cikin kiran da ya yi cewa, ya yaba da fahimtar da shugaban Amurka ya yi cewa, Isra’ila za ta ci gaba da ‘yancin yin aiki da ita, a cewar ofishin Netanyahu.
Firaministan Lebanon Najib Mikati ya ce, tsagaita buɗe wuta wani muhimmin mataki ne na maido da kwanciyar hankali a yankin.
Da yake gode wa Faransa da Amurka kan shigar da suka yi, Mikati ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa na “ƙarfafa ƙarfin sojojin a kudancin ƙasar.”
Iran, mai mara wa Hezbollah da Hamas baya, ta yi maraba da kawo ƙarshen “ta’addanci” da Isra’ila ta yi a Lebanon, bayan da yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta ta fara aiki.
A cikin wata sanarwa da kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Esmaeil Baghaei, ya fitar ya ce, “Maraba da labarin” kawo ƙarshen hare-haren da Isra’ila ke kai wa Lebanon, yana mai jaddada goyon bayan Iran ga gwamnatin Lebanon da al’ummar Lebanon.
Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ta yi maraba da yarjejeniyar, inda ta yaba da yarjejeniyar a matsayin “hanyar da ake wa kyakyawan fata ga ɗaukacin yankin.”
A cikin wata sanarwa da Baerbock ya fitar, ya ce “Mutanen ɓangarorin biyu na kan iyaka suna son rayuwa cikin aminci kuma mai dorewa.”
Firayim Ministan Biritaniya Keir Starmer ya yaba da yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta da aka daɗe ba a gama ba wacce za ta “samar da wani sauƙi ga fararen hula” na Isra’ila da Lebanon.
Da yake kira da a mayar da tsagaita buɗe wuta a ƙasar ta Lebanon, Starmer ya sha alwashin kasancewa kan gaba wajen ƙoƙarin karya lagon tashe-tashen hankula da ake ci gaba da yi a ƙoƙarin samar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin gabas ta tsakiya.
Shugabar ƙungiyar Tarayyar Turai Ursula ɓon der Leyen ta yaba da “labari mai matuƙar kwarin gwiwa” na tsagaita buɗe wuta, tana mai cewa hakan zai ƙara samun “tsaro da kwanciyar hankali a cikin Lebanon.”
Sanarwar abin marhabin ce “musamman ga al’ummar Lebanon da Isra’ila da faɗan ya shafa,” inji ɓon der Leyen ta wallafa a shafinta na ɗ.
Ta ce, Lebanon za ta samu damar ƙara tsaro da kwanciyar hankali a cikin gida sakamakon raguwar tasirin Hizbullah.
Wani babban jami’in Majalisar ɗinkin Duniya ya yi maraba da yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta, sai dai ya yi gargaɗin cewa “akwai jan aiki a gaba” don tabbatar da yarjejeniyar.
“An samu jajircewa, da cikakkiyar goyon baya daga ɓangarorin biyu tadda ake buƙata,” inji jami’ar Majalisar ɗinkin Duniya ta musamman kan Lebanon, Jeanine Hennis-Plasschaert a cikin wata sanarwa.