Sin ta ƙara bai wa Zimbabwe allurar rigakafin COVID-19

Daga CMG HAUSA

Jiya Jumma’a, agogon ƙasar Zimbabwe, ƙasar Sin ta mika ƙarin allurar rigakafin cutar COVID-19 ga Zimbabwe, inda jakadan ƙasar Sin dake Zimbabwe ya bayyana cewa, a halin yanzu ƙasashen biyu wato Sin da Zimbabwe suna gudanar da haɗin gwiwa a tsakaninsu yadda ya kamata, kuma nan gaba za su ƙara haɓaka haɗin gwiwa a fannoni daban daban.

Yawan rigakafi na wannan karo ya kai miliyan 3, uwar gidan shugaban ƙasar Sin Xi Jinping Peng Liyuan ce ta jagoranci aikin, wanda zai samar da allurar miliyan 1 ga mata da matasa da yara na ƙasar Zimbabwe domin taimaka musu a fannin kandagarkin cutar.

Yayin bikin miƙa alluran, uwar gidan shugaban ƙasar Zimbabwe Auxillia Mnangagwa ta sake nuna godiya ga ƙasar Sin saboda tallafin da take samarwa ƙasarta, inda ta bayyana cewa, Zimbabwe ta samu sakamako mai gamsarwa wajen daƙile yaduwar annobar, bayan da ta yi amfani da allurar rigakafin ƙasar Sin.

Kana tana fatan za a ƙara zurfafa haɗin gwiwar dake tsakanin ƙasashen biyu, tare kuma da godewa ƙasar Sin saboda rawar da take takawa kan ci gaban tattalin arzikin Zimbabwe.

Hakazalika jakadan ƙasar Sin dake Zimbabwe Guo Shaochun ya ce, yawan allurar rigakafin da ƙasar Sin za ta bai wa Zimbabwe a bana zai kai miliyan 10, kawo yanzu ta samu alluran da suka kai miliyan 5 daga ƙasar Sin.

Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa