Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Dubun wani matashi mai suna Yahaya Manu, ɗan kimanin shekaru 28, da ya ke zaune a garin Koko na Jihar Kebbi ta cika, inda masu tsaron maƙabartar garin Koko suka kama shi yana tonon kabarin wata mata mai suna Malama Kulu, ’yar kimanin shekaru 64 da aka binne ranar Alhamis 27 ga Oktoba, 2022.
Wakilin Blueprint Manhaja ya yi tattaki zuwa garin na Koko kuma ya zanta da Malam Abdullahi Idris Koko, ɗaya daga cikin masu hidima a maƙabartar, wanda kuma su ne suka kama wannan mutumin.
Ya bayyanawa Blueprint Manhaja cewa, ranar wata Juma’a kimanin sati huɗu da suka wuce ne wannan matashi mai suna Yahaya Manu Koko ya zo maƙabartar da misalin ƙarfe 5:00 na yamma, amma da ya ke akwai damar ziyara a irin wannan lokacin, sai babu wanda ya ce da shi uffan, illa sai dai akan dasa ido ga duk wanda ya shigo maƙabartar.
Saboda haka ana kallon sa ya je wajen da ake ajiye kayan aiki da suka haɗa da kwasa (fartanya), shebur, magini da dai kayan haƙar kabari, ya ɗauki kwasa ya je ya ajiye a kusa da wani sabon kabari ya fita abinsa.
Can kusan ƙarfe 11:00 na dare sai ya sake dawowa, amma wannan lokacin bai ce wa kowa komai ba, haka ya wuce ciki. Bayan wani lokaci da aka fahimci ba wani ne ya rasu ba, sai aka umarci waɗansu da su zagaya ta baya, waɗansu kuma su bi sawunsa.
Yayin da aka je, sai aka tarar yana tonon wani kabari na wata mata da aka binne. Daga nan shi kuma sai ya fita da sauri, amma mutanen da ke ƙofar shiga maƙabartar suka dakatar da shi.
Daga nan sai ya soma zage-zage yana cewa babu uban da ya isa ya hana shi zuwa ziyara, duk da ya ke kowa ya san an hana ziyarar maƙabartar daga ƙarfe 6:00 na yamma.
Daga nan dai da ya ga mutane sun taru akansa, sai ya nemi ya gudu, amma dai aka kama shi.
Ya ƙara da cewa, a lokacin da wannan abin ya faru, akwai aƙalla mutane 30 a ƙofar shiga maƙabartar kuma tare da su aka samu aka kama shi lokacin da ya yi ƙoƙarin ya gudu kuma dukkansu a shirye su ke da su bayar da shaida idan har hakan ta taso.
Hon. Aminu Garba Koko shine Shugaban Ƙaramar Hukumar Koko. Ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya bayyana wa Wakilin Blueprint Manhaja cewa, tuni an hannanta shi wanda ake tuhuma a gaban kotu kuma suna biye da shari’ar har zuwa yadda za ta kaya.
Ya ƙara da cewa, a matsayinsa na shugaban al’umma, ya zama wajibi ya kare mutuncinsu da kuma bibiyar haƙƙoƙinsu.
“Saboda haka ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba wajen bibiyar wannan shari’ar, duk da ya ke waɗansu suna ta yaɗa raɗe-raɗin cewa, wai wanda ake tuhumar yana da tavin hankali, amma dai dukkanmu ’ya’yan garin Koko ne, ba wanda bai san wani ba. Kowa ya san kowa. Saboda haka muna nan muna bibiyar wannan shari’ar har zuwa ƙarshe,” inji shi.
Bayanai da wakilinmu ya tattara daga waɗansu maƙotan wanda ake tuhumar duk da ya ke dai sun ƙi amincewa da a zayyana sunayensu, suna nuni da cewa, ba su san shi da tavin hankali ba, saboda ba ɓoyayyen mutum ba ne a garin Koko ba.
Yana sana’ar acava kuma yana da babura da ya sayar wa waɗansu, ana yi masa haya da su kuma babu wani tarihi da ke bayyana yana da taɓin hankali.
Bayanai sun tabbatar da cewa, da farko dai shi wanda ake tuhumar, wato Yahaya Manu Koko, ya karɓi laifin da ake tuhumarsa, amma daga baya sai wani maƙocinsu mai suna Malam Danjuma Isah Koko ya taimaka musu wajen nemo takarda daga asibitin mahaukata, wanda zai iya sauƙaƙa masa hukunci ko kuma kai wa ƙarshen shari’ar ba tare aiwatar masa da hukunci ba.
Wakilinmu ya nemi jin ta bakin Yahaya Manu Koko, wanda ake tuhuma, sai dai akwai wani maƙocinsu mai suna Malam Danjuma Isah Koko, wanda ake zargin yana zaman sojan haya da ’yan uwansa suka ɗauka, don tsaya masa wajen ba shi kariya a cikin shari’ar, ya hana wakilin namu zantawa da shi a harabar kotun, inda ya ce, “ba mu yarda da ya yi magana da kowane ɗan jarida ba.”
Sufeton ’Yan Sandan Nijeriya Haruna Alfa ya nuna rashin gamsuwar rundunar ’yan sanda da wata takarda da wanda ake tuhumar ya gabatar a matsayin shaidar yana da taɓin hankali daga asibitin mahaukata na Kware, saboda ba a bi hanyar da ta kamata ba wajen samun ta.
Saboda haka Alkali Shehu Abubakar Bada na Babbar Kotun Musulunci da ke garin Koko bayan sauraron ɓangarorin, ya bayar da umarnin aiwatar da ƙwaƙƙwaran bincike kuma bisa ga ƙa’ida, kamar yadda hukuma ta aminta tun daga mataki na farko kafin cigaba da shari’ar.
Malam Aminu Alkali Koko, mai kimanin shekaru 70, shi ne mijin Marigayiya Malama Kulu. Ya bayyana wa Blueprint Manhaja cewa, shi ba abinda ya ke buƙata wanda ya wuce a hukunta mai laifin, saboda ya zama izina ga waɗansu, domin idan ba a hukunta masu irin wannan ta’annati ba, zai saka zukatan duk wanda ɗan uwansa ya ke kwance a maƙabarta zaman ɗar-ɗar, saboda tunanin bayan an binne shi ana iya zuwa a ɗebi waɗansu sassan jikinsa, wanda hakan na iya sanya mutane su daina kai ’yan uwansu da suka rasu maƙabartar.