Sin ta harba kumbon Tianzhou-5 na dakon kayayyaki zuwa samaniya

Daga CMG HAUSA

Da ƙarfe 10:03 na safiyar yau Asabar ne ƙasar Sin ta yi nasarar harba kumbon dakon kayayyaki mai suna Tianzhou-5, wajen aikewa da kayayyaki zuwa tashar sararin samaniya ta ƙasar, wadda ake fatan kammalar ta zuwa ƙarshen shekarar nan.

Hukumar lura da ayyukan saman jannati ta ƙasar Sin ko CMSA, ta ce an harba kumbon ne ta amfani da rokar Long March-7 Y6, daga cibiyar harba taurarin dan adam ta Wenchang, dake lardin Hainan na kudancin ƙasar Sin.

CMSA ta ce bayan mintuna 10 da harba kumbon, Tianzhou-5 ya rabu da rokar Long March-7 Y6, ya kuma shiga falakin sa cikin nasara. Ba da jimawa ba, faifan makamashin hasken rana dake jikin kumbon ya buɗe, tare da fara aiki yadda ya kamata.

CMSA ta ce an kammala aikin harba kumbon cikin nasara.

Daga baya, kumbon ya haɗe da tashar samaniya ta Tiangong. Wannan ne karon farko da ‘yan sama jannati da ke cikin tashar binciken samaniya da Sin ke ginawa suka ga isar kumbon dakon kayayyaki.

Mai fassara: Saminu Alhassan