Sin ta kira taron tattauna mummunan tasirin da manufar mulkin mallaka ya haifar ga haƙƙin bil Adama

Daga CMG HAUSA

Yayin taro karo na 50 na majalisar kula da kare haƙƙin Bil Adam ta MƊD, tawagar dindindin ta ƙasar Sin a ofishin MƊD dake Geneva, ta kira taron tattauna mumunan tasirin da manufar mulkin mallaka ta haifar ga haƙƙin bil Adam ta kafar bidiyo.

Chen Xu, Wakilin dindindin na tawagar ƙasar Sin dake ofishin da sauran ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa dake Switzerland, ya bayyana cewa, kamata ya yi ɓangarori daban-daban su duƙufa kan kawar da mumunan tasirin da manufar mulkin mallaka ya haifar musamman ma a fannin haƙƙin bil Adam, ta yadda za a tabbatar da adalci a duniya da ingiza bunƙasar aikin kare haƙƙin bil Adam.

Farfesa a kwalejin shari’a ta jami’ar Wuhan ta ƙasar Sin, Zhang Wanhong da masana daga Afrika ta Kudu da Indiya da Zimbabwe, sun bayyana ra’ayoyinsu a fanonnin da suka yi nazari game da mumunan tasirin tsarin mulkin mallaka, inda suka bayyana cewa, Amurka da Birtaniya da sauran ƙasashen Turai, sun jefa mutanen da suka yiwa mulkin mallaka cikin masifa, saboda irin kisan ƙare dangin da suka yi musu. Amma, wadannan ƙasashe ba su dubi laifufukan da suka aikata ba, inda suke ci gaba da tsoma baki kan harkokin cikin gidan sauran ƙasashe bisa fakewa da batun haƙƙin bil Adam.

Kuma suna amfani da ƙarfinsu a fannin tattalin arziki da tsare-tsaren da suka kafa, wajen ware ƙasashe masu tasowa daga tsarin tattalin arzikin duniya ta hanyar fakewa da batun haƙƙin bil Adam da ƙwadago da ma’aunin muhalli da sauransu, ta yadda za su ci gaba da kwashe makamashi da ci da guminsu.

Fassarawa: Amina Xu