Sin ta yi nasarar harba samfurin ɗakin gwajin tashar binciken sararin samaniya na Mengtian

Daga CMG HAUSA

Da yammacin yau ne ƙasar Sin ta yi nasarar harba ɗakin gwaje-gwaje na biyu na tashar binciken sararin samaniyarta da ake kira Mengtian zuwa sararin samaniya, matakin dake ƙara kusanto ga aikin kammala tashar ya zuwa ƙarshen wannan shekara.

Da misalin ƙarfe 3 da mintuna 37 agogon Beijing ne, aka harba samfurin ɗakin gwajin na Mengtian ta hanyar amfani da rokar Long March-5B daga cibiyar harba taurarin ɗan-Adam dake Wenchang na lardin Hainan dake kudancin ƙasar Sin.

Mai fassarawa: Ibrahim