Ƙasar Sin za ta ƙara buɗe ƙofarta ga ƙasashen ƙetare

Daga CMG HAUSA

A game da shakkun da ƙasashen ƙetare ke nunawa game da batun buɗe ƙofar ƙasar Sin ga kasashen waje, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yayin taron manema labarai da aka saba shiryawa Litinin din nan cewa, buɗe ƙofa ita ce babbar manufar ƙasar Sin.

Rahoton babban taron wakilan JKS karo na 20, ya bayyana ƙarara game da inganta buɗe ƙofa ga ƙasashen ƙetare, inda ya nuna cewa, ya kamata a inganta matakin haɗin gwiwar cinikayya da zuba jari.

Wannan ya ƙara nuna cikakken ƙudirin ƙasar Sin na buɗe ƙofa ga ƙetare bisa babban mataki.

Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa