Shirin ƙidaya: NPC ta ƙaddamar da shafin intanet don ɗaukar ma’aikata

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa (NPC), ta ƙaddamar da shafinta na intanet don ɗaukar ma’aikatan wucin-gadin da za su taya ta aikin shirin ƙidaya mai zuwa.

Shugaban hukumar, Honarabul Nasir Isa-Kwarra ne ya jagoranci ƙaddamar da shafin a matsayin wani mataki na shirye-shiryen shirin ƙidaya ‘yan ƙasa da hukumar za ta gudanar a Afrilun 2023.

Yayin da yake jawabi a lokacin ƙaddamar da shafin ranar Litinin a babban ofishin hukumar da ke Abuja, Isa-Kwarra ya ce ma’aikatan da za a yi amfani da su wajen gudanar da shirin, za a zaɓo su ne daga mazauninsu.

Ya ce dabarar yin hakan shi ne, don rage wa gwamnati kashe kuɗaɗe wajen jigilar ma’aikata zuwa sassan ƙasa daban-daban.

Ya ƙara da cewa, hakan kuma zai ba wa jama’a damar ba da tasu gudunmawa ga shirin a yankunansu ta hayar tabbatar da an ƙidaya kowa da ke yankin nasu.

A cewarsa, domin cimma kyakkyawan sakamako dangane da shirin, dole ana buƙatar ma’aikata da yawa.

Kazalika, ya ce ƙoƙarin da hukumar ke yi na tabbatar ta yi aiki da gaskiya kuma mai tsafta, shi ya sa ta ƙaddamar da shafin ɗaukar ma’aikata don kowa ya shiga ya gwada sa’arsa.