Buhari ya tafi London duba lafiyarsa

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya tafi London domin duba lafiyarsa kamar yadda ya saba.

Sanarwar tafiyar Buhari na ƙunshe ne cikin sanawar da mai bai wa Shugaban Ƙasa Shawara, Femi Adesina ya fitar ranar Litinin.

Adesina ya ce Buhari ba zai dawo Nijeriya ba sai a mako na biyu na watan Nuwamban 2022.

Kimanin watanni shida kenan da Buhari ya yi makamancin wannan tafiya zuwa London bisa dalili na kula da lafiya.

Shugaba Buhari ya fara tafiya London ne watanni takwas bayan lashe zaɓen 2015 inda ya shafe kwana shida, wato daga 5 zuwa 10 ga Fabrairu, 2016.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *