Ƙungiyar Izala za ta haɗa kai da gidauniyar Zakka a Gombe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) reshen Jihar Gombe ƙarƙashin shugabancin Injiniya Salisu Muhammad Gombe da shugaban Majalisar Malamai Sheik Abubakar Lamido Abubakar, ta yi alkawarin haɗa kai da Gidauniyar Zakkah da Wakafi don gudanar da aikace-aikacen tare.

Shugaban ƙungiyar Izala, Injiniya Salisu Muhammad Gombe, ya bayyana hakan ne a lokacin ziyarar da suka kai ofishin gidauniyar da ke harabar tsohon Masallacin Modibbo Bubayero da ke fadar jihar.

Ya ce, maƙasudin ziyarar tasu shi ne bayyana kansu ga shugabannin gidauniyar su kuma sanin manufofi da aikace-aikacenta don ganin ta inda ƙungiyar za ta shigo domin yin haɗin gwiwa.

Ya ƙara jinjina wa gidauniyar bisa ga irin ayyukan madalla da ta yi wajen bada tallafi ga marasa galihu da kuma yadda take raba zakah a jihar.

A nasa jawabi tun farko, shugaban gidauniyar, Ustaz Abdullahi Abubakar Lamido, ya jinjina wa ƙungiyar ta Izala sannan ya ce za su ci gaba da yin ayyuka tare da ita da sauran ƙungiyoyi.

Lamido, ya yi alƙawarin bai wa ƙungiyar gurbin samun horo a gidauniyar ta zakka da wakafi da ta ke gudanarwa.