Sinima ta na ƙarfafa haɗin-kan al’umma – Ministar Al’adu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ministar Ma’aikatar Al’adu, Hannatu Musa Musawa ta ce sinimar haska finafinai ta na ɗaya daga cikin ginshiƙan da ke ƙarfafa haɗin-kan al’ummar ƙasa.

A lokacin da ta ke jawabi a bikin finafinan Zuma na Ƙasa da ƙasa (ZUFF) karo na 14 a Abuja, Musawa ta ce fim wani fage ne na musamman da ke inganta haɗin-kai acikin mutanen da suka zo daga ɓangarori daban-daban.

Taron ZUFF na wannan shekarar an fara shi tun a ranar 1 ga watan Disamba wanda a yau ne ake ƙarƙare shi, ya bayyana yadda harakar fasaha ta sa sinima ta ƙasaita.

Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkar ingantayya, Mista Prince Baba Agba shi ya wakilci ministar a taron inda ta nuna damuwa kan cimma muradin gagarumin bikin na ‘Destination Nigeria 2030’.

Ta ƙara da cewa, sinima aba ce da ke haɗe kan mutane mabanbanta ta hanyar bayyana kai da kuma ilmantar da juna game da al’adu da harkokin yau da kullum.

A nasa jawabin, Darakta-Manaja na Hukumar Finafinai ta Ƙasa (NFC), Dakta Ali Nuhu, ya bayyana sinima a matsayin wajen musayar al’adu da kawo sauye-sauye acikin al’umma.

Ali Nuhu, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin shirya taron, ya ce sinima a Nijeriyance ta wuce nishaɗi, ta kai matakin haɗaka wajen bayyana tarihi a tsakanin mutane mabanbanta da kuma ƙarfafa haɗin-kai.

Ya kuma bayyana yadda fasahar zamani ta taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin ƴan fim a Nijeriya da masu kallo, wanda zai taimaka wajen ɗaukaka muryar Nijeriya a ko’ina a faɗin duniya.

By Babaji