Mataimakin Gwamna tare da wasu fasinjoji sun tsallake rijiya da baya

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Mataimakin gwamnan Jihar Borno, Umar Kadafur, tare da wasu fasinjojin jirgin Max Air, sun tsallake rijiya da baya sakamakon lalacewar jirgin da suke ciki.

Wakilin mu ya rawaito cewa mataimakin gwamnan yana daga cikin mutane 100, da suke cikin jirgin na Max, lokacin da jirgin ya samu matsala sakamakon kamawa da wuta da injin jirgin yayi jim kaɗan bayan tashi daga filin tashi da saukar jiragen saman ƙasa da ƙasa na Maiduguri a jiya Laraba.

Lamarin wanda ya faru da misalin ƙarfe 7 na daren Laraba yayin da jirgin ya ɗauki hanyar zuwa birnin tarayya Abuja.

Injin jirgin dai ya kama da wuta mintuna 10 da tashi, wanda bugar wani tsuntsu da ya yi ta kawo masa matsalar.

Bayan haka, an umarci matuƙin jirgin ya gaggauta dawowa filin jirgin na Maiduguri don kiyaye afkuwar hatsarin da ka ’iya janyo asarar rayuwar al’umma.

Da yake tabbatar da lamarin, wani ma’aikacin kamfanin Max Air ya ce, jim kaɗan bayan tashin jirgin ya bugi tsuntsu a cikin iska, wanda ya sa ɗaya daga cikin injunan sa ya kama wuta.

Sannan yace matuƙin jirgin ya yi aiki cikin gaggawa don tabbatar da lafiyar dukkan fasinjoji.

Manhaja Blueprint ta riwaito cewa Kamfanin na Max Air dai yayi gaggawar samarwa da fasinjojin wani jirgin don kai su inda suka yi niyyar zuwa, yayin da wasu fasinjojin suka koma gida.

By ukarofi