SOAR ta horar da masu fafutukar kare haƙƙin jinsi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wata ƙungiya mai zaman kanta ‘Sexual Offense Awareness and Response Initiative’, ta ce, ta horar da mutane aƙalla 257 a matsayin maza masu fafutukar kare haƙƙin jinsi a sansanonin ‘yan gudun hijira daban-daban (IDP) a Benuwai.

Jami’in shirin na ƙungiyar, Mista Chibuzor Njoku ne ya sanar da hakan a taron kwamitin aiwatar da haƙƙin ƙananan yara na Benuwai a ranar Alhamis.

Chibuzor ya bayyana cewa, an yi wannan horon ne akan dandamalin shirin samar da shawarwarin samari na yaƙi da cin zarafin mata da ayyukan Y-map.

Ya ci gaba da cewa, wani shirin – Girls Empowerment Mentoring Programme (GEMS Arise) – ya horar da yara mata da uwaye matasa aƙalla 381 da suka rasa matsugunansu a matsayin masu ba mata shawara a sansanonin ’yan gudun hijira.

Wani wanda yake kishin lalata da yara ya kafa shirin wayar da kan jama’a kan Laifukan Jima’i a cikin 2011 don hanawa da kuma magance yawaitar cin zarafin yara da mata.

A halin yanzu dai ƙungiyar na aiki da wani shiri na magance aurar da yara ƙanana a yankin Arewa ta tsakiyar ƙasar.

An sadaukar da ita don rigakafin duk nau’ikan cin zarafin yara tare da ba da kulawa da tallafi ga waɗanda abin ya shafa da waɗanda suka tsira.