
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Dakarun tsaro na Atisayen Haɗin Kai a Arewa maso Gabashin Nijeriya, sun yi nasarar halaka wasu ‘yan ta’adda a lokacin da suka daƙile wani hari da mayaƙan ISWAP suka yi yunƙurin ƙaddamarwa a sansanin sojoji da ke yankin Gajiram a Ƙaramar Hukumar Nganzai ta Jihar Borno.
Jami’in Hulɗa da jama’a na rundunar na riƙo, Kyaftin Mohammed Goni, wanda ya sanar da haka a wata takarda da ya fitar a ranar Litinin, ya ce wani adadi mai yawa na ‘yan ta’adda ya ƙaddamar da mummunan farmaki a sansanin dakarun na sansanin FOB a Gajiram da misalin ƙarfe 12:20 na daren ranar da nufi lalata tsarin tsaron sojojin, lamarin da ya sanya dakarun tsaron suka mayar da martani cikin hanzari.
A cewarsa, a musayar wuta da aka yi tsakanin ɓangarorin biyu, sojoji sun nuna fin ƙarfi akan ‘yan ta’addar, wanda hakan ya yi sanadiyyar halaka da dama daga cikinsu da raunata wasu da kuma janyewa daga yunƙurin farmakin nasu.
Haka kuma, nasarar daƙilewar ta yi sanadin dakarun sun ƙwato wasu muggan makamai, alburusai da kuma na’urorin sadarwa.
Goni ya ƙara da cewa, wani faifan bidiyo da aka samu bayan ba-takashin ya nuna yadda mayaƙan suke janye ‘yan uwansu da aka raunata ko halaka yayin da suke ja da baya, kuma ana gudanar da bincike kan makaman da aka ƙwato daga wajen maharan.
Saidai, ya ce wasu sojoji sun jikkata sakamakon samun raunukan harbin bindiga yayin daƙile harin mayaƙan, sannan wasu makamai da motocinsu sun lalace sakamakon harbo makamin gurnet.
A cewarsa, tuni aka garzaya da jami’an da suka jikkata zuwa wajen karɓar magani, inda ake ba su kulawa, yayin da wasu dakarun ke cigaba da sintiri a sassan daban-daban na kewayen yankin don bayar da kariya ga yiwuwar fuskantar wani yunƙurin harin ‘yan ta’addar.
