
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Dakarun tsaro na Atisayen Haɗin Kai a Arewa maso Gabas, sun yi nasarar kama wani da ake zargin ɗan tsegumi ne ga ƙungiyar ISWAP bisa zargin wani shiri na kai farmaki ga sansanin sojoji guda biyu a Jihar Borno.
Rahotanni sun bayyana cewa, Muhammad Shuaibu ne sunan wanda ake zargin, wanda dakarun Bataliya ta 212 da ke sansanin ayyuka (FOB) na yankin Chabbol suoa yi ram da shi bayan samun wani bayanin sirri akan shirin ƙaddamar da farmakin.
Wata majiyar sojoji ta shaida wa manema labarai cewa, an kama Shuaibu ne yayin wani sintiri da jami’an tsaron suka gudanar daga tazarar mita 500 daga wajen da aka jibge motocin kariyar sansanin.
Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin na da alaƙa da mummunan hare-haren da aka shirya ƙaddamarwa akan jami’ai na musamman na Bataliya ta 199 da ake kira da Mosquito Camp da kuma FOB a Chabbol.
Haka kuma, wanda ake zargin ya ƙara da cewa, mayaƙan suna da nufin ƙaddamar da atisayen koda kuwa an kama shi yayin shirin nasu.
A cewar sojoji, kamen ya sa dakarun sun ɗauki matakin ƙarfafa tsaro a yankunan daga dukkan wani yunƙuri na kai hari.
Tuni dai aka miƙa Shuaibu ga sashen leƙen asiri na sojoji domin cigaba da gudanar da bincike akansa.
