Sojoji sun ceto mutum 16 a hannun ‘yan bindiga a Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Jami’an soji dake da sansani a Marabar Mai-Gora sun samu nasarar ceto waɗansu mutane da ‘yan bindiga suka sace tare da yin garkuwa da su tun kimanin kwanaki 46 da suka wuce.

Waɗanda lamarin ya shafa sun haɗa da mata 10 da kuma ƙananan yara shida.

Sojoji sun taki wannan nasarar ce a lokacin da suke gudanar da sintiri a garin Rimi.

Wadanda aka ceto ɗin, na daga cikin mata 54 da barayin daji suka sace a hanyar Gamji zuwa Ɗandume a farkon watan Fabarairun da ya gabata.

Sakataren yaɗa labarai na gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Muhammad Kaula, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya yaba wa tawagar sojin da suka gudanar da wannan aikin .

Ya ce, “Ceto waɗannan mata da yaransu ya tabbatar nuna jajircewa da jarumtar jami’an tsaro.

“Gwamnati za ta ci gaba da samar masu da kayan aiki gami da ba su goyon bayan da suke buƙata don tabbatar da tsaron al’umar jihar.” Inji sanarwar.

Tuni aka miƙa waɗan aka ceto ɗin ga shugaban Ƙaramar Hukumar Sabuwa, inda shi kuma ya sake miƙa su ga iyalansu.

By Editor