Daga BASHIR ISAH
Kwamitin Majalisar Wakila kan yaƙi da zazzaɓin Maleriya, HIV/AIDS da Tarin Fuka, ya bai wa Ministan Lafiya, Farfesa Mohammed Ali Pate, sa’o’i 72 kan ya bayyana a gabanta ko kuma ta sa a kamo shi.
Gayyatar ta shafi har da Babban Sakatariyar Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, wato Daju Kachollom.
Majalisar ta buƙaci Pate da Kachollom su abayyana a gabanta ne domin amsa tambayoyi kan zargin karkatar da Dala miliyan 300 da aka ware domin yaƙi da zazzaɓin maleriya tun daga 2021.
Kwamitin ya yanke shawara kan cewar a damƙo Babbar Sakatariyar muddin ta ƙi amsa gayyata, saboda a cewarsa, a baya ma ta ƙi amsa gayyata.
Kwamitin ƙarƙashin jagorancin Hon Amobi Godwin Ogah, ya nuna rashin jin daɗinsa da rashin ganin Sakatariyar duk da gayyatar da ya tura mata.
Ogah ya ce: “A halin da ake ciki, maleriya ta zama annoba a Nijeriya. Sau da dama gwamnati na son taimaka wa jama’a, amma ma’aikatan gwamnati ne matsalarmu.
“An tanadi wannan kuɗi tun a shekarar 2021. Ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, mun tura wa Sakatariyar da gayyata.
“Wannan shi ne karo na uku da muke gayyatar ta a kan ta zo ta yi mana bayanin abin da ya faru.
“Shin sun yi amfani da kuɗin daka ware? Idan kuwa ba su yi amfani da su ba, ina kuɗaɗen suke? Abu ne da ke buƙatar bayani cikin sauƙi.
“Amma sai faman gudu suke yi, sannan suna turo mana jama’a daban-daban kan su yi mana magana, sai dai mun zo nan ne domin kare ‘yan Nijeriya.
“An zaɓe mu ne domin mu wakilci mutanenmu. Ba zai yiwu mu zuba ido muna kallon maleriya na yi wa ‘yan Nijeriya ɗauki ɗai-ɗai ba,” in ji shi.
