Daga USMAN KAROFI a Abuja
Sojojin Operation FANSAN YANMA sun daƙile jerin hare-haren da ‘yan bindiga suka kitsa a ƙananan hukumomi daban-daban na Jihar Katsina. Jami’an tsaron sun hana sace mutane a wurare uku a cikin ƙaramar hukumar Ɗandume: Unguwar Iidi, Albasu a kan hanyar Tumburkai da kuma Unguwar Hawan Idi. An fara harin da misalin ƙarfe 12:25 na tsakar dare ranar Lahadi, inda sojoji suka mayar da martani cikin gaggawa, suka fafata da maharan har suka tilasta su guduwa cikin daji.
A yayin wannan artabu, wani mutum mai suna Malam Sale ya samu rauni sakamakon harbin bindiga, kuma aka garzaya da shi zuwa Asibitin Gwamnati na Ɗandume domin samun kulawa.
Duk da haka, wani mazaunin unguwar, Malam Auwalu, ya ɓata bayan an kwantar da tarzoma. Jami’an tsaro sun fara aikin nema da ceto domin gano inda yake. Wannan matakin ya nuna yadda sojojin ke ƙara zage damtse wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a a yankin.
A wani aiki na daban da aka gudanar a ƙaramar hukumar Matazu, jami’an tsaro sun ceto wani dattijo mai shekara 60, Alhaji Abdullahi Mohammadu Bello, wanda shi ne Wakilin Hakimin Matazu.
An sace shi a ranar Asabar amma aka kuɓutar da shi da misalin ƙarfe 4:00 na yamma a ranar Lahadi a ƙauyen Maharba. Bayan an ceto shi, an kai shi asibitin koyarwa na Tarayya da ke Katsina domin duba lafiyarsa, daga bisani kuma aka mayar da shi cikin iyalansa.
Hukumomin tsaro sun tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike don gano waɗanda suka aikata laifukan da kuma karɓar bayanai daga wurare daban-daban.
Wannan nasara ta nuna irin kulawar da hukumomin tsaro ke nunawa wajen kare lafiya da kwanciyar hankalin al’ummar Jihar Katsina, tare da tabbatar da cewa jami’ai na cikin shirin ko da yaushe don tunkarar barazana.
