
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Dakarun tsaro sun yi nasarar halaka mayaƙan Lakurawa guda biyu yayin da suka farmaki wata daba ta ‘yan ta’addar a Ƙaramar Hukumar Tangaza da ke Jihar Sakkwato.
Haka kuma sun ƙwato wasu muggan makamai da dabbobi da aka sace a wasu atisayen a jihohin Sakkwato da Katsina.
A cewar wata sanrwa da Mataimakin Daraktan hulɗa da jama’a na riƙo na rundunar da ke sashe na 8 kuma ɓangare na 2 na atisayen FANSAN YAMMA, Laftanal Kanal Olaniyi Osoba ya fitar a yau Juma’a, atisayen, wani ɓangare ne na yaƙi da ayyukan ‘yan ta’adda da ɓarayin daji a shiyyar Arewa ta Yammacin Nijeriya.
Osoba ya ce, dakarun sun amsa wani kiran gaggawa ne akan yunƙurin wasu da ake zargin Lakurawa ne na cinna wa wani yankin Hukumar Shige da Fice wuta a ƙauyen Ruwa Wiri da ke Tangaza.
Ya bayyana cewa, an yi ba-takashi tsakanin sojojin da maharan, wanda ya sa aka halaka mayaƙan biyu, yayin da sauran suka tsere saboda fin ƙarfi da dakarun suka nuna musu.
Ya ƙara da cewa, bayan haka an ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda biyu da tarin alburusai da kuma babur ɗaya.
A wani labarin kuwa, dakarun tsaro a Ƙaramar Hukumar Jibiya da ke Katsina, sun yin nasarar karɓe wasu dabbobi da ɓarayin daji suak sato a yankin Ɗanya Bakwai.
A yayin haka ne ‘yan ta’addar suka tsere saboda ganin ƙarfin farmakin sojojin, waɗanda daga bisani suka damƙa wa masu dabbobi dukiyoyinsu a fadar dagacin Daddara da ke ƙaramar hukumar.
