Daga JOHN D WADA a Lafia
Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya sanar da cewa an kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyya APC mai ci a jihar domin kujerun majalisar wakilai na tarayya wanda aka shirya za a gudanar a ranar Juma’a15 ga Mayu na shekarar 2026 da ake ciki a jihar.
Gwamna Sule ya bayyana hakan ne yayin da yake wa manema labarai jawabi a sakatariyar ƙungiyar manema labarai ta ƙasa (NUJ) reshen jihar da ke Lafia babban birnin jihar.
An wakilce gwamnan a taron ta hannun mataimakin sa na musamman kan harkokin hulɗa fa jama’a Hon. Peter Ahemba wanda ya bayyana cewa wannan zaɓe zai fitar da ‘yan takar jam’iyyar domin zaɓen 2027 na ƙasa baki ɗaya.
Ahemba ya ce kawai masu kaɗa ƙuri’a dake da katin mamba na jam’iyya wanda aka sanya wa tambarin hukuma ne za a bar su shiga zaɓen fidda gwanin.
A cewarsa zaɓen fidda gwanin na majalisar wakilai zai gudana ne a hedkwatar kowace mazaɓar tarayya a faɗin jihar.
“Wannan an yi shi ne domin tabbatar da cewa tsarin ya kasance cikin sauƙi kuma wakilai su samu damar zuwa wuraren zaɓe cikin sauƙi a mazaɓunsu,” in ji shi Peter Ahemba.
Ya ƙara da cewa an kammala dukkan shirye-shiryen da ake buƙata a wuraren da aka ware domin tabbatar da gudanar da zaɓen cikin nasara.
Ahemba ya kuma tabbatar da cewa jam’iyyar ta APC ta shirya sosai domin zaɓen fidda gwanayen nata inda ya ƙara da cewa za a kuma tura jami’an tsaro a faɗin jihar domin tabbatar da gudana cikin lumana.
Haka kuma ya bayyana cewa jerin sunayen da za a yi amfani da su a zaɓen shi ne wanda jam’iyyar da hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) suka amince da shi.
