
Daga BELLO A. BABAJI
Hedikwatar Tsaron Nijeriya, DHQ, ta ce an kama jami’ai biyu na tawagar ‘hybrid forces’ bisa laifin yin aiki tare da ƴan ta’adda a Shiyyar Arewa maso Gabashin Nijeriya.
Daraktan Harkokin yaɗa Labarai, Manjo-Janar Markus Kangye ya faɗi hakan a wata takarda, ƙarshen mako.
Ya bayyana cewa, jami’an suna daga cikin hybrid forces da aka ware don yi aiki da sojoji wajen daƙile ayyukan ta’addanci a shiyyar.
Ya ce, an kama su ne a yayin atisayen da aka gudanar a ranakun 26 zuwa 29 na watan Afrilu, 2025 a Ƙananan Hukumomin Bama, Kukawa da Madagali.
Manjo Janar Kangye ya ƙara da cewa, jami’an suna daga cikin guda huɗu da ke kai wa ƴan ta’addar da aka kama kayan aiki, ya na mai alla-wadai da hakan a matsayin butulci ga aikin soja.
Ya kuma yi kira ga kwamandodi da su riƙa Ilimantar da jami’ai game da haɗarin da ke tattare da haɗa kai da ƴan ta’adda wanda ka iya zama barazana ga ƙoƙarinsu na daƙile ayyukan ta’addanci.
