Tsohon shugaban ƙaramar hukumar Zamfara ya koka kan hare-haren ‘yan bindiga

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD Gusau

Tsohon shugaban ƙaramar hukumar Anka Hon. Mustapha Gado Anka ya bayyana damuwarsa kan hare-haren da ‘yan ta’adda suke kai wa al’ummar garin Anka a Jihar Zamfara.

Hon. Mustapha Gado Anka ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da yayi da Blueprint Manhaja yau Lahadi ta wayar tarho.

A cewarsa, ‘yan bindigar sun addabi garin, suna kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, tare da yin garkuwa da wasu da dama a kusan kullum.

“A yayin da nake magana da kai da rana tsaka yau waɗannan ‘yan ta’addan da suka addabi al’ummar mu sun kai hari a sakatariyar ƙaramar hukumar mu, inda suka kashe wani Alhaji Kabiru Danbuga Mai Aski tare da yin garkuwa da wani Yazidu Muhammad”. Yace

A cewarsa rashin isassun jami’an tsaro a yankin shi ne ya fi ɗaukar hankalin al’ummar yankin.

“Rashin isassun jami’an tsaro don daƙile waɗannan ‘yan ta’addan dake kai hari a ƙaramar hukumar mu ta Anka shi ne babban ƙalubalen mu”. Yace

Hon. Gado Anka ya zargi gwamnatin tarayya da nuna halin ko-in-kula kan matsalar rashin tsaro a Jihar Zamfara, inda ya ƙara da cewa a halin yanzu ‘yan bindiga na yawo cikin walwala da muggan makamansu a garin Anka ba tare da wata matsala ba.

“Yan ta’addan yanzu a halin da muke ciki suna shigowa garin Anka ɗauke da makamansu ba tare da wata tangarɗa ba, kuma a kowane lokaci suna kai wa mutanen mu hari lamarin da ke haifar da rashin tabbas ga mutanenmu”. Inji Hon Gado

Ya kuma buƙaci gwamnatin tarayya da ta tura ƙarin sojoji yankin da kuma yaƙi da ‘yan ta’adda da suke gurgunta duk wani ci gaban tattalin arzikin yankin.

“Dole ne gwamnatin tarayya ta yi duk abin da ya kamata don magance matsalar rashin tsaro da ya addabi yankinmu da kuma yankin Arewa maso Yamma gaba ɗaya domin a samu zaman lafiya”. Yace

Hon. Mustapha Gado Anka Ya yabawa gwamnatin Jihar Zamfara a ƙarƙashin jagorancin gwamna Dauda Lawal bisa jajircewar da ya yi wajen magance matsalar rashin tsaro da ke addabar jihar.

“Ina son in yabawa gwamnatin Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin gwamna Dauda Lawal bisa damuwarsa kan rashin tsaro da ya addabi jiharmu”. Hon. Gado Anka ya nuna

By ukarofi