Wararrun ‘yan majalisar dokokin Zamfara sun sha alwashin kare muradun mazaɓarsu

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD Gusau

Wararrun ‘yan majalisar dokokin Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Hon. Bashar Aliyu Gummi Sun yi alƙawarin ci gaba da gudanar da ayyukansu a matsayinsu na masu bin doka da oda don kare haƙƙin al’ummar mazaɓar su .

Hon. Aliyu Ango Kagara
Mamba mai wakiltar mazaɓar Talata Mafara ta kudu ya bada wannan tabbacin a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Gusau yau Lahadi.

A cewarsa, babu wata barazana daga ɓangaren gwamnatin jihar da zai iya kawo cikas ga shugabancin da suke da shi.

“Muna sane da farautar da gwamnatin jihar ke yi akan mu kuma mun rubuta koke kan gwamnatin Dauda Lawal ga hukumomin tsaro a matakin jiha da na ƙasa.” Ya kuma ƙara da cewa.

Ya kuma nuna fargaba kan shirin da wasu ‘yan bangar siyasa na kusa da gwamnatin jihar sukayi don kai musu hari, inda ya ce sun sanar da jami’an tsaro kan lamarin domin kare lafiyarsu.

A cewarsa, gwamnatin jihar na shirin bai wa wasu tsoffin shugabannin majalisar dokokin jihar umarnin ganawa da su don ganin an shawo kan rikicin dake tsakanin su, ya ƙara cewa matsalar su na gaban kotun ɗaukaka ƙara da ke Sakkwato.

Ya zargi gwamnatin jihar da yin amfani da wata ƙaramar kotu domin neman a kama su ba tare da wani tuhuma ba, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Halima Jaafar Mikaila.

Ya nanata cewa matsayarsu kan mutunta doka da duk wani ɓangare na gwamnati a jihar yananan daram. Yana mai jaddada cewar basa tsoron duk wata barazana, kuma ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen gudanar da aikin su.

By ukarofi