APC a Zamfara ta caccaki gwamnatin jihar kan cin zarafin ‘yan majalisar dokoki

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD Gusau

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen Jihar Zamfara, ta gargaɗi gwamnatin Jihar Zamfara da ta guji farautar ‘yan majalisar dokokin jihar guda tara da suka ware domin nemawa kansu yancin dimukraɗiya.

Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na jihar Yusuf Idris ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Gusau yau Lahadi.

Jam’iyyar ta zargi ofishin gwamna Dauda Lawal ta hanyar yin amfani da babbar majistire ta ɗaya, ƙarƙashin mai Shari’a Halima Jaafar Mikaila wajen bayar da umarnin a kamo ‘yan majalisar guda tara ba tare da sammaci ba.

“Mu a jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara abun damuwa ne da abin matuƙa yadda gwamnatin jihar ke amfani da ɓangaren shari’a wajen kai farmaki ga zaɓaɓɓun ‘yan majalisar dokokin jihar da kundin tsarin mulki ya zaɓa domin gudanar da ayyukansu na majalisa”.

“Duk da cewa ana shari’a a kotun ɗaukaka ƙara dake Sokoto, kotun majistare ta ci gaba da bayar da umarnin a kamo ‘yan majalisar ba tare da wata tuhuma ko kuma gayyata ba”. Sanarwar ta bayyana

Jam’iyyar ta yi kira ga gwamnatin jihar a ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal da ta daina tsangwamar ‘yan majalisar ba tare da sasanta rikicin dake tsakani ba.

“Ko shakka babu jam’iyyar APC za ta ci gaba da kasancewa a ɓangaren doka kuma ba za ta bari a riƙa siyasantar da ɓangaren shari’a ba da amfani da su wajen saɓawa muradun jama’a. Yusuf yace

Jam’iyyar ta yi nuni da cewa, za ta bijirewa duk wani yunƙuri na yi wa ‘yan majalisar karan tsaye don kawai sunyi bayanin yanayin tsaron dake damun mazaɓunsu daban-daban.

Jam’iyyar ta shawarci ‘yan majalisar da su kai ƙorafi ga hukumar shari’a ta Ƙasa kan abin da ta bayyana a matsayin kotu na siyasantar da lamarinsu ba bisa ƙa’ida ba a jihar .

By ukarofi