
Daga Sanusi Muhammad a Gusau
Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta 1 Brigade da Sector 1 Joint Task Force (North West) Operation Hadarin Daji (OPHD) a ƙarƙashin ‘Operation Sahel Sanity II’, sun yi nasarar kashe ƴan bindiga biyu a ƙoƙarin da sojojin ke yi na samun nasarori a yaƙin da su ke yi da ƴan bindiga a jihar Zamfara.
Daraktan hulɗa da jama’a na1 Brigade/Sector 1 OPHD, Lt Suleiman Omale ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da aka rabawa Blueprint ranar Asabar.
“A ranar 16 ga watan Agustan 2024, sojojin bisa umarnin kwamandan runduna ta 1 na sojojin Najeriya da kuma sashin 1 na haɗin gwiwa (Arewa-maso-Yamma) Operation Hadarin Daji, Birgediya Janar TM Opurum sun yi nasarar kashe ƴan bindiga biyu a wani ƙazamin arangama da suka yi a Unguwar Sarkin Musulmi ta ƙaramar hukumar Ƙaura Namoda.”
“Aikin sahihan bayanan sirri, sojojin galant sun hanzarta mayar da martani ga rahotannin ayyukan ta’addanci a yankin kuma da isowarsu, sun shiga cikin ‘Element’ a cikin wani mummunan harin bindiga tare da kawar da biyu daga cikin masu tsattsauran ra’ayi.”
A cewarsa, an tilastawa sauran ƴan fashin janyewa cikin ruɗani yayin arangamar.
Laftanar Omale ya cigaba da cewa, sojojin sun gudanar da wani samame inda suka ƙwato babur guda ɗaya na ƴan ta’addar.
Ya yi nuni da cewa, tun daga lokacin, an tabbatar da tsaro a yankin, tare da dakarun haɗin gwiwa na Sector 1 Joint Task Force (Arewa-maso-Yamma) Operation Hadarin Daji, suna ci gaba da kai farmaki tare da gudanar da sintiri na ƙarfafa gwiwa domin tabbatar da tsaron lafiyar al’ummar yankin.
Nasarar da aka samu na wannan aiki na nuni da yadda rundunar Operation Hadarin Daji ke cigaba da ƙoƙarin kawar da ƴan bindiga a Zamfara da kuma dawo da zaman lafiya da tsaro a yankin.
