Sojoji sun kashe babban mai yaɗa farfagandar ISWAP da tawagarsa a Borno

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar Operation HAɗIN KAI (OPHK) ta sanar da kashe babban jami’in yaɗa farfaganda na ƙungiyar ISWAP, Abu Salim al-Barnawi, tare da wasu mambobin tawagarsa a wani samame da aka kai a Jihar Borno.

A cikin wata sanarwa da Muƙaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na rundunar, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar a Maiduguri, ya ce wannan nasara za ta raunana ƙarfin ISWAP wajen yaɗa farfaganda da kuma ɗaukar sabbin mabiya.

Sanarwar ta bayyana cewa Abu Salim tsohon kwamandan ISWAP ne kafin daga bisani a mayar da shi shugaban sashen yaɗa labarai na ƙungiyar, inda yake jagorantar ɗaukar bidiyo, hotuna da kuma shirya saƙonnin farfaganda da ƙungiyar ke yaɗawa.

A cewar rundunar, an kashe Abu Salim tare da wasu daga cikin manyan abokan aikinsa, ciki har da Abu Umar Khattab da Abu Khalid Usman, yayin da suke ƙoƙarin kai hari kan wani sansanin sojoji da ke Cross Kauwa a Jihar Borno a ranar 12 ga Yuli, 2026.

Bayan artabun, dakarun sun ƙwato kyamarar ɗaukar bidiyo da wasu kayayyakin da ake zargin tawagar yaɗa labaran ISWAP ke amfani da su wajen shirya farfaganda.

Rahotannin leƙen asiri sun kuma nuna cewa Abu Salim ya taɗa jagorantar hare-hare zuwa ƙasar Kamaru kafin daga bisani a sauya masa aiki zuwa sashen yaɗa labarai na ƙungiyar.

Rundunar ta ƙara da cewa an kashe wasu mayaƙan ISWAP da dama a harin, ciki har da wani kwamanda mai suna Aliyu Zabarmari, yayin da har yanzu ba a tantance inda wani mayaƙin haya ɗan ƙasar Larabawa yake ba.

A cewar OPHK, mutuwar waɗannan manyan jami’ai za ta raunana tsarin jagoranci da yaɗa farfagandar ISWAP, tare da rage ƙarfin ƙungiyar wajen yaɗa saƙonninta.

Rundunar ta kuma bayyana cewa ISWAP ta fitar da sanarwar mutuwar Abu Salim, abin da ta ce ya tabbatar da rasuwarsa.

Operation HAɗIN KAI ta jaddada kudirinta na ci gaba da kai hare-hare da gudanar da ayyukan leƙen asiri domin tarwatsa hanyoyin sadarwa da tsarin yaɗa farfaganda na ƙungiyoyin ’yan ta’adda, tare da tabbatar da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas

By ukarofi

Leave a Reply