Sojoji sun soma gudanar da bincike a kan kisan Janar Ahmed

Daga UMAR M. GOMBE

Sojojin Nijeriya tare da haɗin gwiwar takwarorinsu sun soma gudanar da bincike domin gano ‘yan bindigar da suka kashe Manjo Janar Hassan Ahmed kwannan nan a Abuja.

Jami’an sun soma binciken ne a yankin Koton Ƙarfe a jihar Kogi.

An yi zargin wasu ‘yan bindiga ne daga Koton Karfe suka harbe marigayin a kan hanyarsa ta komawa Abuja daga jihar Kogi.

Yayin harin ‘yan bindigar sun tafi da wata ‘yar’uwar marigayin wadda suke tare da ita a cikin motarsa, yayin da direbansa kuwa ya tsallake rijiya da baya.

A juma’ar da ta gabata aka yi jana’izar Manjo Hassan a maƙabatar sosoji da ke Barikin Lungi a Abuja.

Bayanai sun nuna Koton Ƙarfe na daga cikin yankunan da suka yi ƙaurin suna wajen harkokin ‘yan bindiga da garkuwa da mutane da sauran muggan laifuka.