Sojoji sun hallaka mai kai wa su Turji makamai a Shinkafi

Daga BASHIR ISAH

A wani samame da Rundunar Mayaƙan Sama ta Nijeriya (NAF) ta kai da jirigin yaƙinta a Jihar Zamfara, Rundunar ta samu nasarar kashe Malam Ila wanda ya yi ƙaurin suna waje safarar makamai a ƙauyen Manawa cikin Ƙaramar Hukumar Shinkafi a jihar.

Majiyar PRNigeria ta ce, Ila shi ne babban mai yi wa ‘yan ta’adda safarar makamai, musamman ma Bello Turji a Zamfara.

Majiyar ta ce, “A ranar 18 ga Nuwamban 2022 NAF a ƙarƙashin Operation Hadarin Daji suka kai samamen inda aka hallaka Malam Ila.

“Malam Ila ya kasance wanda ake nema ruwa a jallo saboda kusancinsa da kwamandojin ‘yan bindigar irin su Bello Turji da Ɗan Bokoyo.

“Yaransu ne ke da alhakin kai hare-hare a yankin Shinkafi a Jihar Zamfara da wasu sassan jihohin Kaduna da Neja da Kebbi da kuma Sakkwato.

“Bayan jefa makamai da jirgin ya yi, an ga aukuwar fashewa da dama wanda hakan ke nuni da lalata wasu muggan makaman ‘yan bindigar ke da su ɓoye a yankin.”

Mai magana da yawun NAF, Edward Gabkwet, ya tabbata da faruwar hakan. Tare da cewa, jami’an tsaro za su ci gaba da aikin bankaɗo harkokin ‘yan bindigar a jihar ta Zamfara.