Jami’ar Jihar Kwara ta yi babban rashi

Daga BASHIR ISAH

Allah Ya yi Mataimakin Shugaban Jami’ar Jihar Kwara (KWASU), Muhammed Akanbi, rasuwa.

Marigayin wanda farfesa ne a fannin doka kuma Babban Lauyan Nijeriya (SAN), ya bar duniya yana da shekara 51.

Rijistaran jami’ar ya tabbatar da rasuwar marigayin cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi da daddare.

“Cikin alhini da sadaukarwa ga Allah, Hukumar Gudanarwar ta Jami’ar Jihar ke sanar da rasuwar Mataimakin Shugaban jami’ar, Farfesa Muhammed Mustapha Akanbi SAN,” inji sanarwar.

An naɗa marigayi Akanbi a matsayin Mataimakin Shugaban KWASU ne a watan Afrilun 2020.

Marigayin ɗa ne ga shugaban hukumar ICPC na farko, marigayi Mustapha Akanbi.

Kafin rasuwar, marigayin ya yi fama da rashin lafiya tun daga 2020 inda sai a wannan lokaci rai ya yi halinsa.

Tuni Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya aika da saƙon ta’aziyyarsa ga ahalin marigayin.