Muhammad Isa shi ma ya amsa kiran mahalicci

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Ana cikin juyayin rasuwar tsohon editan jaridar LEADERSHIP, Danladi Ndayebo sai kuma ga mutuwar abokin tafiyarsa Muhammad Isa.

Wallahi abin juyayi ne aiunun. Idan ana bin labaru Danladi Ndayebo ne ya sanar da cewa sun yi hatsari kan hanyar zuwa Minna aj jihar Neja kuma a lokacin Muhammad Isa ya fi jin jiki.

Labaru na nuna lokacin da marigayi Ndayebo ya bugo waya ɗan jarida Abdul’aziz Abdul’ziz don neman taimakon turo mota a kai su asibiti, an ji sautin Kalmar shahada da ya tabbatar Muhammad Isa ne da ke mawuyacin yanayi a loakcin.

Hatta shi kan sa Ndayebo ya nuna Muhammad Isa na neman taimako na musamman kenan don garzayawa da shi asibiti. Cikin ikon Allah sai a ka wayi gari da jin Danladi Ndayebo ne ya rasu. Lokaci ya yi babu dabara.

Sannan sai jama’a su ka shiga ta’aziyyar Allah ya jikan Ndayebo ya kuma ba wa Muhammad Isa lafiya. Cikin ƙwarin guiwa har ma Muhammad Isa na iya buga waya da karanta saƙonnin gaisuwar fatan alheri.

Inda ma kowa zai tabbatar da haka sai an shiga shafin fesbuk na marigayin za a ga inda ya yi godiya da kan sa ga waɗanda su ka jajanta ma sa kan hatsarin da miqa ma sa ta’aziyyar mutuwar abokinsa Ndayebo.

Marigayi Muhammad Isa har ma ya bayyana cewa ya na samun sauƙi. Gabanin nan akwai wani sako da ya rubuta da harshen Turanci ya na mai cewa, ‘LOGGING OUT FOR NOW, SO LONG’ wato ma’ana bari in rufe ko in dakata a nan, lokaci ya yi tsawo!

Ashe bankwana marigayin ya ke yi kuma sai Allah kaɗai ya san wane nazari ya yi ya rubuta waɗannan kalmomi masu haruffa 22. Babban ɗan jarida Ibrahim Sheme ya zayyana kalaman da hango ƙaddarerren abun da zai faru kamar yadda ya rubuta da Turanci ‘SO PROPHETIC’.

Duk da haka don kwantarwa mutane hankali marigayin ya fitar da sanarwar ƙarshe ta nuna ya na samun sauƙi. Dama haka rayuwa ta ke kuma daga ganin labarin rasuwar bayan na nazarci lamarin sai na fara wannan rubutu a tsarinb rubuta labari kamar haka “’Yan kwanaki kalilan bayan rasuwar tsohon editan jaridar LEADERSHIP Danladi Ndayebo a sanadiyyar hatsarin mota, shi ma abokin tafiyarsa Muhammad Isa ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayi Ndayebo da Muhammad Isa na kan hanyar zuwa Minna a jihar Neja lokacin da su ka samu hatsarin kuma ba a daɗe ba Danladi Ndayebo da ya ba da labarin hatsarin ya rasu, inda shi kuma Muhammad Isa da ya fi jin jiki a zahiri ya yi ’yar jinya kafin Allah ya karɓi abinsa.

Tuni shafukan sada zumunta su ka cika maƙil da masu isar da sakwan ta’aziyya da zayyana Muhammad Isa da mutum mai zumuncin gaske.

Marigayi Muhammad Isa na aiki ne a majalisar dokokin Nijeriya inda ya ke lamuran da su ka shafi taimakawa ta fuskar yaɗa labaru.

A lokacin da wannan hatsari ya afku kan hanyar Minna jihar Neja har hakan ya yi sanadiyyar rasuwar abokan aiki, hakanan wani hatsrin a daidai lokacin ya yi sanadiyyar rasuwar abokin ’yan jarida Sarkin Arewan Bauchi Alhaji Hassan Sharif.

Hatsarin ya afku ne shi kuma kan hanyar zuwa Abuja a Akwanga jihar Nasarawa. Allah bai ƙaddari marigayin zai iso Abuja ba don sai juyawa da shi a ka yi Bauchi a ka yi masa jana’iza a fadar mai martaba Sarki.

Hatsari ba ya hana sake shiga mota a cigaba da tafiya. Ma’ana ba hatsari ne hanyar mutuwa ba a’a ƙaddara ce ko sanadi. Shi mai rai lalle wataran sai ya ɗanɗani mutuwa ko da kuwa yana zaune lami lafiya a gida ne.

Ku duba ma na da zarar afkuwar hatsarin su Ndayebo ai mota a ka nema don kai su asibiti. Kazalika shi ma na Sarkin Arewa motar a ka sake ɗauka a ka juya da shi Bauchi. Da farko ma kamar yadda labarin ya zo, jami’an kiyaye afkuwar hatsari ba su bayyana cewa marigayi Alhaji Hassan Sharif ya rasu ba.

Har ma na saurari hira da ɗaya daga ’ya’yan sa da ke magana kan hanyar tafiya Akwanga don duba halin da mahaifin su ya ke ciki da bayyana babu tabbacin rasuwar. Jami’ai su kan ɓoye labari mai razanarwa har sai a hankali in an zo a fahimta.

Hatsarin mota na daga hanyoyin da a kan samu asarar rayuka a Nijeriya. Zai yi wuya mutum ya ɗauki babbar hanya ya yi tafiyar kilomita 100 bai ga inda a ka samu hatsarin mota ba ko da kuwa hatsarin ba a ranar ya afku ba.

Hanyoyin mota a Nijeriya in ban da kalilan na cike da ramuka da in tsautsayi ya zo sai ka ga an samu fashewar taya. Hakanan za ka taras ko wani direba na tafiya cikin natsuwa sai a samu wani sarkin gaggawa ya wuce fuuuu da gudu ko ya saka kai inda bai dace ba har a iya samun taho mu gama.

Hanya mai layi ɗaya zuwa da dawowa kan zama nan ne manya da ƙananan motoci ke bi. Ga shi kuma wasu wajajen da kwanoni masu tsanani ko hawa da gangara.

A ’yan shekarun nan kuma direbobi da dama kan so saurin wuce wasu wajaje a dazuka don kasancewar wajajen masu hatsari da fargabar fitowar varayi masu satar mutane don karɓar kuɗin fansa.

Rashin ingantattun hanyoyin sufuri sun sa titin mota ne a Nijeriya ke ɗaukar rinjayen fasinjoji masu tafiya a dukkan faɗin jihohin ƙasar 36 da Abuja. An samu koma baya ma kan titin jirgin ƙasa don yadda a ’yan watanni ’yan ta’adda su ka kai hari kan jirgin ƙasa da ya kama hanya daga Abuja zuwa Kaduna har a ka samu asarar rayuka da sace mutane duk Allah ya hukunta duk masi sauran shan ruwa ya koma gida.

Wannan ƙalubale zai zama darasi ta hanyar da za a dau matakai da amfani da labarun sirri wajen kare matafiya. Kazalika ya na da kyau a cigaba da shimfiɗa titunan jirgin ƙasa a duk faɗin Nijeriya don talakawa da ba za su iya biyan dubban kuɗi a jirgin sama ba, su samu hanya mai sauƙi ta yin tafiye-tafiyensu.

Wata shawara ma ya na da kyau gwamnatin tarayya da haɗin guiwar gwamnatocin jihohi ta ƙarfafa kafa tashoshin hutawar matafiya ko madakatar manyan motoci kamar yadda hukumar kasauwancin jiragen ruwa ta fara kafawa a wasu sassa da ba mu da tabbacin ko sun fara aiki a irin Tafa, Ogbulafor, Potiskum da sauran su.

In mun yi la’akari da hatsarin da ya afku da su Ndayebo, sai da ya ɗaure da kansa ya buga waya don a kawo mu su ɗauki da hakan ya nuna ba madakatar binciken jami’an tsaro kusa ko wata cibiya ko ma ƙauye da za a iya kawo agajin gaggawa.

Idan duk a kilomita 100 za a kafa wata madakata mai ɗakin kula da majinyata na gaggawa, wajen cin abinci da kama ruwa zai taimaka ainun da tabbatar da cewa gwamnati na kula da lafiyar jama’ar ta.

Zan tuna gamuwa ta ta ƙarshe da Muhammad Isa wata rana ce bayan babbar sallar nan ta 2022 na zo ofishin mu na Muryar Amurka a Abuja kuma lokacin shugaban sashen Hausa Aliyu Mustapha Sokoto ya na ziyarar aiki.

Na shigo na samu ya na tare da baƙo. Ina son shiga don mu yi magana da Alhaji Aliyu amma na lura su na magana mai muhimmanci kan lamuran yau da kullum da baƙon.

Bayan dogon lokaci na ga ya dace na leƙa don ganin muhimmin baƙo da ya ke tare da shugaban VOA HAUSA har na tsawon lokaci alhali ga mutane na jiran ganawa da shi da sauran ayyuka masu tarin yawa.

Ina shiga na yi sallama a ka amsa abun da zan iya tunawa sai kawai na ji an ce ‘EL-HIKAYA DA MA INA NEMAN KA’ ashe marigayi Muhammad Isa ne! Nan mu ka yi ta magana kuma bai ma daɗe ba ya yi sallama da Alhaji Aliyu mu ka fito harabar ofishin har inda ya ajiye motarsa mu ka sake kafa majalisar hira kan muhimman abubuwan rayuwa.

Inda na tsinke da lamarin marigayin yayin da na tambayi ya ba ni lambarsa, sai kawai ya ce ya na da lamba ta bari ya bugo min kuma haka a ka yi. A ɗan ƙanƙanin lokaci ya yi bayanai masu gamsarwa da sharhi kan lamuran siyasar 2023.

In ka ji ya na magana ka san ya san abun da ya ke faɗa don ba shaci faɗi a bayanansa. Wallahi wani abu da na lura da shi shi ne ba shi da wuce gona da iri ko karambani. Na kara sakankancewa da fassarar tawa lokacin da nag a ta’aziyyar da shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya yi wa iyalan marigayin.

Kasancewar Muhammad Isa mai taimakawa Sanata Lawan ne kan labaru. Cikin abun da Sanata Lawan ya zayyana har da kwarewar marigayin kan aiki da kuma nuna cewa ba a tava samunsa da sakaci da aiki ba.

Kammalawa;

Mutuwa babban wa’azi ne ga waɗanda su ke raye don kuwa ba makawa za a mutu kuma duk yanda mu kan rubuta labarin mutuwar wasu mu ma haka wataran zai kasance.

Ina addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya jikan marigayan nan da magabatan mu iyaye da kakanni; mu kuma da mu ka rage Allah Ya sa mu gama da duniya lafiya.