Bayan tilasta biyan ‘Kuɗin Kariya’, ’yan bindiga sun wawushe mutum 44 a ƙauyen Zamfara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Aƙalla mutum 44 ne ’yan bindiga suka yi awon gaba da su a ƙauyen Kanwa da ke Ƙaramar Hukumar Zurmi ta Jihar Zamfara.

Mazauna yankin sun ce maharan sun yi wa ƙauyen ƙawanya ne cikin dare, inda suka riƙa bi gida-gida suna kwasar mutane, galibi mata da ƙananan yara.

A baya-bayan nan dai, an ɗan sami salamar yawan satar mutane a ƙauyukan Zamfara, amma bisa ga dukkan alamu a ’yan kwanakin nan, cikin mazauna ƙauyukan ya fara ɗurar ruwa saboda yadda lamarin ya sake dawowa.

Ana dai zargin cewa riƙaƙƙen ɗan bindigar nan na yankin, Dankarami ne ya shirya satar mutanen, wanda yana daga cikin ’yan ta’addan da sojoji ke neman ruwa-a-jallo.

Dankarami dai ya jima yana addabar mazauna yankunan Zurmi zuwa Birnin Magaji zuwa Jibiya a kan iyakar jihohin Zamfara da Katsina.

A wani labarin kuma, mazauna garin Moriki sun fara yin ƙaro-ƙaro domin tara Naira miliyan 20 a matsayin ‘Kuɗin Kariya’ da ’yan bindiga suka buƙata daga wajensu.

A cewar mazauna yankin, ana bi gida-gida ne domin tattara kuɗin da za a kai wa ’yan ta’addan da ke ƙarƙashin Bello Turji.

Ɗan ta’addan da tawagarsa dai sun yi alƙawarin cewa za su kare yankin daga mahara matuƙar aka ba su kuɗin kamar yadda suka buƙata.

Garin Moriki dai wanda ke kan hanyar Shinkafi zuwa Kauran Namoda ya sha fama da hare-hare a baya, ciki har da na sace wani malami a wata makarantar sakandaren ’yan mata da ke garin.