‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 20 a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

‘Yan bindiga a Jihar Zamfara,sun sace mutum 20 ciki har da wasu tagwaye ‘yan mwana huɗu da haihuwa.

Wannan na zuwa ne jim kaɗan bayan da Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Ibrahim Dosara, ya bayyana cewa an inganta tsaro a jihar.

Garkuwa da mutanen ta faru a garin Daura cikin Ƙaramar Hukumar Zurmi a jihar.

Wani mazaunin garin, Malam Haruna Ahmad Dauran, ya tabbatar wa Blueprint Manhaja aukuwar hakan a tattaunawar da suka yi ranar Lahadi.

A cewarsa, ‘yan bindigar sun mamaye garin ne da misalin ƙarfe 8:30 na safiyar Asabar inda suka fara bincike gida-gida inda suka yi awon gaba da mutanen.

Haruna ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi yunƙurin kai wa masu ibada a cikin Masallaci hari amma sai suka tsere yayin harin.

Ya bayyana cewa, yawancin waɗanda abin ya shafa matan aure ne.

“Maganar da nake yi da kai yanzu, kashi casa’in na waɗanda aka sace mata ne da suka haɗa da tagwaye ‘yan kwana huɗu tare da mahaifiyarsu,” inji shi.

Ya kuma bayyana cewa, ‘yan bindigar sun kai hari ƙauyen Baichin Dauran a lokacin da suka kai harin.

A cewarsa, “Lokacin da al’ummar ƙauyen Baichin Dauran ke shirin binne gawar ɗan uwansu da ‘yan ta’addar suka hallaka, a safiyar jiya Asabar, ‘yan bindigar sun tare su a babbar maƙabartar garin tare da ƙwace wayoyinsu da kuɗaɗe da ba a bayyana adadinsu ba.”

Haruna ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Zamfara da su kawo musu agaji, kuma su daina siyasantar da matsalar tsaron jihar.

“Abin da ya sa nake kira ga gwamnatin Jihar Zamfara da ta daina sanya siyasa kan harkokin tsaron jihar shi ne yadda gwamnati ta bakin Kwamishinan Yaɗa Labaran jihar, Ibrahim Dosara ta fitar da wata sanarwa a yau cewa tsaro ya inganta a jihar wanda hakan ba gaskiya ba ne,” inji Haruna.

Ya zuwa haɗa wannan labari, babu wani cikakken bayani daga rundunar Rundunar ‘Yan Sandan jihar kan wannan batu.