Sin ta kafa sabon bajinta a fannin ƙara ingancin batir ta Silicon mai amfani da hasken rana

Daga CMG HAUSA

Cibiyar nazarin makamashin hasken rana ta ƙasar Jamus (ISFH) ta ba da sabon rahoto cewa, batirin silicon mai amfani da hasken rana da kamfanin Sin ya ƙirƙiro, yana iya juya hasken rana zuwa wutar lantarki da kashi 26.81%, wanda ya kasance matsayin ƙoli a duniya a wannan fanni.

An ba labari cewa, jigon ci gaban fasahar amfani da ƙarfin hasken rana shi ne inganta aiki na juya ƙarfin hasken rana zuwa wutar lantarki da rage farashin wutar lantarki.

Batir ɗin da Sin ta ƙirƙiro a wannan karo yana da ingancin aiki matuƙa.

Rahotanni na cewa, ƙasar Sin ta kafa wannan bajimta ne bisa batir din dake iya amfani da hasken rana wajen samar da wutar lantarki na kashi 26.7 da ƙasar Japan ta ƙirƙiro a shekarar 2017, shekaru 5 da suka gabata, Sin ta kafa wani sabon bajimta, kuma shi ne karon farko da kamfanin Sin ya kafa bajimta a wannan fanni.

Mai fassara: Amina Xu