Wang Yi: Ziyarar Xi a ƙetare na nuni da yadda Sin ta himmatu wajen samun cigaban duniya

Daga CMG HAUSA

Mamban majalisar gudanarwar ƙasar Sin kana ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi, ya bayyana cewa, halartar taron ƙolin G20 karo na 17, da taron shugabannin haɗin gwiwar tattalin arziki na ƙasashen yankin Asiya da tekun Fasifik karo na 29, da kuma ziyarar aikin da ya kai kasar Thailand, na nuni da cewa, ƙasar Sin za ta ci gaba da sa ƙaimi ga tabbatar da zaman lafiya da ci gaban duniya, da ƙara buɗe ƙofa da yin hadin gwiwa.

Wang ya shaida wa manema labarai cewa, sanin kowa ne cewa, a cikin gida da kuma waje a gabar da duniya ake fuskantar wani yanayi mai sarkakiya, ta hanyar sa ƙaimi ga bunkasuwar duniya da tafiyar da harkokin ƙasa da ƙasa, ƙasar Sin ta nuna rawar da take takawa a matsayinta na babbar ƙasa.

Ya jaddada cewa, yayin ziyarar da ya kai ta kwanaki 6, shugaba Xi ya halarci ayyuka fiye da guda 30, da ƙoƙarin ganin an raya da jagorancin tafiyar da harkoki na duniya, da nuna matsayin ƙasar Sin a matsayin babbar ƙasa mai riƙon amana da sanin ya kamata.

A yayin da yake jawabi ga taruka masu nasaba da ɓangarori daban-daban da dama da kuma tattaunawa da shugabannin wasu ƙasashe kuwa, shugaba Xi ya yi karin haske kan sakamakon babban taron wakilan JKS karo na 20 da ya kammala cikin nasara, da batun zamanantar da ƙasar Sin, da hadin gwiwar samun nasara tare tsakanin Sin da ragowar ƙasashen duniya.

Wang ya ƙara da cewa, ana sa ran ƙasar Sin za ta samu ci gaba mai inganci da buɗe ƙofa ga ƙasashen ƙetare.

Yana mai nuni da cewa, ƙasar Sin za ta ci gaba da inganta zaman lafiya da ci gaban duiya, da zurfafa buɗe ƙofa da yin hadin gwiwa da ragowar ƙasashen duniya.

Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa