Sojoji sun tarwatsa maɓuyar ‘yan fashin daji a Kaduna

Sakamakon ruwan bamabamai da sojoji suka yi wa ‘yan fashin daji a Zamfara wanda ya yi sanadiyar halaka da damansu a ‘yan kwanakin nan, hakan ya rutsa da wata maɓuyar ɓarayin a jihar Kaduna.

Bayanan da MANHAJA ta kalato sun nuna maɓuyar da sojojin suka tarwatsa a dajin Kawara a yankin ƙaramar hukumar Igabi, nan ne ‘yan bindigar kan ɓoye suna gudanar da harkokinsu na takura wa al’umma.

Kamar yadda bayanai suka tabbatar, a ƙalla ‘yan bindiga 50 ne aka kashe sakamakon ruwan bamabamai da sojoji suka yi wa maɓuyar tasu a ƙarshen makon da ya gabata.

An bayyana cewa a wannan rana, a daidai lokacin da jirgin yaƙin sojojin ke shawagi sai ya hangi ‘yan fashin a maɓuyar tasu inda su kuma suka yi ƙoƙarin ɓoyewa cikin garken shanun da suka sato a dajin Kawara.

Daga bisani bayan da ɓarayin suka kora shanun kuma a daidai inda suka nemi tsallake ruwa, a wannan wuri ne jirgin ya samu zarafin fatattakar su.

Bayan bincike da tattara bayanai, an tabbatar da an samu gawarwaki a ƙalla guda 50 na waɗanda suka mutu a artabun, haka ma an lalata kayan abinci da babura mallakar ɓarayin.