‘Yan bindiga sun yi garkuwa da ‘yar tsohon daraktan NBC, Abdulkadir a Katsina

A daren Litinin da ta gabata ‘yan bindiga suka kai hari a rukunin gidaje na Bakori a jihar Katsina inda suka sace yarinyar tsohon darakta a hukumar NBC, Alhaji Ahmed Abdulkadir, mai suna Laila.

Haka nan, ‘yan bindigar sun haɗa da wasu mutum uku yayin harin, wato Alhaji Bello Aminu Bakori da Shamsuddeen Aminu da kuma Habibu Rabe suka yi gaba da su.

‘Yan fashin sun kai harin ne da misalin ƙarfe 9 na dare a wannan rana ɗauke da bindigogi ƙirar AK 47.

An ce kimanin ƙasa da awa guda bayan harin, sai aka haɗa kan ‘yan banga don su bi sawun ɓarayin.

Bayanai sun nuna sakamakon ɗauki-ba-daɗin da aka yi tsakanin ‘yan bangan da ɓarayin a yankin ƙaramar hukumar Ɗanja aka samu sa’ar kuɓutar da mutum uku daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su ɗin. Sai dai ba a samu kuɓutar da Abdulkadir da ‘yarsa ba.

Wannan na zuwa ne kimanin sa’o’i 24 bayan da wasu ‘yan fashin daji suka yi garkuwa da iyalan ɗan majalisar dokokin jihar Katsina.

A kwanakin baya-bayan nan, ‘yan bindiga sun matse ƙaimi wajen gudanar da harkokinsu a sassan ƙasa lamarin da ke jefa rayuwar jama’a da dama cikin haɗari da kuma yi wa tsaron ƙasa barazana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *