Sojoji sun yi nasarar kashe kwamandan Bello Turji da wasu ‘yan ta’adda a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Dakarun Operation FANSAN YAMMA sun kashe babban kwamanda kuma na hannun daman fitaccen ɗan ta’addan Bello Turji mai suna Aminu Kanawa.

Sojojin sun kuma yi wa wasu makusantan Bello Turji rauni da suka haɗa da, Dosso (ƙanin Bello Turji) da Ɗanbokolo (ɗaya daga cikin makusantan Turji).

Daraktan yaɗa labarai na ma’iakatar tsaro Manjo Janar Edward Buba ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Gusau yau Laraba.

“Bugu da ƙari, sojoji sun kashe wasu manyan kwamandojin Bello Turji da suka hada da Abu Ɗan Shehu, Jabbi Dogo, Ɗan Kane, Basiru Yellow, Kabiru Gebe, Bello Buba da Ɗan Inna ƙahon Saniya-Yafi-Bahaushe, da sauransu”.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, sojojin sun yi nasarar kashe sama da ‘yan ta’adda 24 da suka tsere daga sansanin Bello Turji da ke kusa da Gebe a ƙaramar hukumar Isa ta Jihar Sakkwato, da kuma kewayen Gidan Rijiya a ƙaramar hukumar Shinkafi ta Jihar Zamfara.

Sojojin sun kuma kashe wani fitaccen ɗan ta’adda a harin da aka kai a unguwar Bello Turji da ke unguwar Fakai mai suna Suleiman, da kuma mai biyayya ga fitaccen shugaban ‘yan ta’adda, Halilu Sububu.

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa shi Suleiman ya jagoranci tawagar da ta taimaka wajen ceto sansanin Bello Turji da ke cikin ruɗani, lokacin da aka yi nasarar kawar da shi a lokacin da aka yi musayar wuta.

Hakazalika rasuwar na hannun damar Bello Turji a matsayin kwamandan kwamandoji da mayaƙa a matsayin wani gagarumin rauni ne ga ƙungiyar ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso yammacin ƙasar nan, da kuma ƙarfinsu na soji da yaƙi.

Waɗannan gungun ‘yan ta’adda sun yi ƙaurin suna wajen yawan garkuwa da mutane da hare-haren ta’addanci a faɗin Arewa maso Yamma, musamman a ƙananan hukumomin Zurmi, Shinkafi, Isa, da Sabon Birni a Jihohin Zamfara da Sakkwato.

A cewar sanarwar, sojojin ba za su ja da baya ba har sai an halaka Waɗannan ‘yan ta’adda gaba ɗaya, tare da lura da cewa ayyukan sojojin na da nufin samar da yanayi na tsaro ga dukkan ‘yan ƙasar.