Sojojin Nijar sun kashe Lakurawa a kan iyakar Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar Sojin Jamhuriyar Nijar ta bayyana cewa jami’anta sun kashe mayaƙan Lakurawa – waɗanda suka shiga ƙasar ta Kudu maso yammaci, kamar yadda kafar Tamtan.info mai zaman kanta ta ruwaito a ranar 25 ga Nuwamba.

Rundunar ta ce sun kashe mayaƙan ƙungiyar a ranar 21 ga Nuwamba a Muntseka, na yankin Illela da ke Kudu maso yammacin jihar Tahoua da ke kan iyakar ƙasa da Nijeriya.

Rahoton ya ƙara da cewa, “‘yan ta’adda ne da ake kira Lakurawa ko Lukurawa da suka ɓulla a jihohin Arewa maso yammacin Nijeriya musamman, Kebbi da Sakkwato da suke da iyaka da jihohin Jamhuriyar Nijar wato Dosso da Tahoua, inda suka kashe mutum 15.

“Wataƙila sun gudu ne daga Nijeriya suka shiga Nijar domin tserewa daga yaƙarsu da sojojin Nijeriya ke yi,” in ji rahoton.

Lakurawa sun ɗauki alhakin wasu hare-hare a jihohin Kebbi da Sakkwat, kuma suna iƙirarin alaƙa da ƙungiyar Ansaru wadda ke samun goyon bayan ƙungiyar al-qaeda.